An yi garkuwa da ’yar ƙasar waje a Nijar

Karo na farko ke nan da aka sace wani ɗan ƙasar waje a Nijar tun bayan da sojoji suka karɓe mulki a Jamhuriyar Nijar.

An yi garkuwa da ’yar ƙasar waje a Nijar

’Yan bindiga a Jamhuriyar Nijar sun yi garkuwa da wata baturiya ’yar ƙasar Austria da ke zaune a yankin Agadez.

Karo na farko ke nan da aka sace wani ɗan ƙasar waje a Nijar tun bayan da sojoji suka karɓe mulki a Jamhuriyar Nijar.

Mazauna da hukumomi sun tabbatar da sace matar, wadda ma’aikaciyar wata ƙungiyar jinƙai ce.

Ma’aikatar Harkokin Wajen ƙasar Austria ta ce ofishin jakadancinta da ke Aljeriya wanda kuma shi ke kula da Shiyyar Jamhuriyar Nijar ta tabbatar da garkuwa da ma’aikaciyar jiƙan mai suna Eva Gretzmacher.

Kafar yada labarai ta Ait Info da ke Agadez ya ruwaito cewa Misis Eva Gretzmacher “sananniya ce wurin aikin taimakon al’umma a yankin Agadez inda ta gina cibiyar koyar da sana’o’i a shekarar 2010. Ta daɗe tana zaune a Agadez kuma ta ba da gudunmawa a fannin raya da tallafa wa mata da raya ilimi da al’adu da kare muhalli da sauransu.”

Kawo ya zu babu wata ƙungiya da ta yi ikirarin sace ’yar ƙasar Austriar kuma hukumomin Nijar ba su fitar da wata sanarwa ba.

Nijar ta shafe shekaru kamar maƙwabtanta Najeriya da Chadi da Burkina Faso da Mali, tana fama da hare-haren ta’addancin ƙungiyoyi masu iƙirarin jihadi.

Gaza magance wannan matsalar na daga cikin dalilan da sojojin ƙasar suka bayan wajen yin juyin mulkin da suka yi wa Shugaba Mohammed Bazoum a shekarar 2023.

Sai dai har yanzu matsalar ta ƙi ci ta ƙi cinyewa, inda wasu ke ganin abin ya ƙara munana.

Nijar ta rasa sojoji da dama a sakamakon wannan matsala, kuma a watannin baya ’yan ta’adda sun kai hari wani babban gidan yari a kasar inda suka saki tsararru da dama, ciki har da abokansa.

Mahara sun kashe mutum 9 sun jikkata wasu a Nasarawa

Aikin titin tiriliyan 16 ya yi layar zana a kasafin 2025

An yi garkuwa da ’yar ƙasar waje a Nijar

Sojin sama sun yi kuskuren kashe mutum 16 a Zamfara