An yi garkuwa da yara 23 a gidan marayu a Kogi

’Yan bindigar sun kutsa cikin makarantar Dahallukitab Group of Schools ne a cikin daren ranar Lahadi, inda suka yi ta harbe-harbe, sa’annan suka yi awon gaba da mutum 26, da suka hada da dalibai 23 da matar shugaban makarantar, wadda ke hade da gidan marayau.

An yi garkuwa da yara 23 a gidan marayu a Kogi

’Yan bindiga sun yi garkuwa da yara 23 a wata makamranta mai hade da gidan marayu a yankin Kabba Junction da ke kan hanyar Lokoja- Okene a Karamar Hukumar Adavi da ke Jihar Kogi.

Rahotanni sun bayyana cewa ’yan bindigar sun kutsa cikin makarantar mai suna Dahallukitab Group of Schools ne a cikin daren ranar Lahadi, inda suka yi ta harbe-harbe, sa’annan suka yi awon gaba da dalibai 23 da matar shugaban makarantar da wasu mutum biyu a makarantar, wadda ke hade da gidan marayau.

Wani mazaunin yankin da ke kusa da garin, ya bayyana cewa, “Abin mamaki ne yadda maharan suka kai farmaki a gidan marayu, inda suka yi ta harbi da misalin karfe 10.30 na dare.

“Da safen nan muke samun labarin cewa ’yan bindigar sun kai hari a gidan marayu da makaranta, inda suka yi garkuwa da yara da kuma matar matar mai makarantar da wasu ma’aikata.”

Gwamnatin Jihar Kogi dai ta tabbatar da aukuwar lamarin, inda ta yi  Allah wadai da shi, ta wata sanarwa da Kwamishinan Watsa Labarai na Jihar Kogi, Kingsley Fanwo, ya fitar.

Amma sanarwar ta safiyar Litinin ta bayyana cewa jami’an tsaro sun yi nasarar ceto mutum 15 daga cikin yaran da maharan suka yi garkuwa da su.

Da yake jinjina wa kokarin jami’an tsaron wajen dakile mummunan tasirin harin, Fanwo ya bayyana cewa ’yan sanda da sauran jami’an tsaro na ci gaba kokarin ceto ragowar mutum 15 da ke hannun ’yan bindigar

Sai dai ya bayyana damwuwa game dayyukan cibiyoyin da ba su da rajista a wurare masu nisa.

Ya gargaji jama’a game da kafa gidajen marayu da makaranut da dangoginsu a wurare masu fama da barazana ba tare da sanar da hukumin da abin ya shafa ba, yana mai cewa hakan yana jefa rayuka cikin hadarin tsaro.

Don haka ya umarci masu bude makarantu da gidajen marayu da su tabbata sun bi duk ka’idojin da ak gindaya tare da bin ta hannun hukumomin da suka dace.

Wakilinmu ya ne samun karin bayani game da harin daga ’yan sanda, amma hakan bai samu ba. Ya kira kakakin ’yan sanda na jihar, ASP Saliu Oyiza Afusat,  ta waya, ya kuma tura masa rubutattun sakonni, amma bai samu amsa ba, har zuwa lokacin da muka kammala wannan rahoton.