An yi gasar kwallon Badminton a Minna

Hukumar Kula da Wasan Badminton ta kasa tana shirye-shiryen horar da matasan da suka samu nasara a gasar wasan Badminton na kasa da aka yi a Kwalejin Horar da Malamai na Jihar Neja. Wannan wani mataki ne a yunkurin zakulo ’yan wasan da za su fafata a gasar Nahiyar Afrika da za a yi nan […]

An yi gasar kwallon Badminton a Minna
An yi gasar kwallon Badminton a Minna

Hukumar Kula da Wasan Badminton ta kasa tana shirye-shiryen horar da matasan da suka samu nasara a gasar wasan Badminton na kasa da aka yi a Kwalejin Horar da Malamai na Jihar Neja. Wannan wani mataki ne a yunkurin zakulo ’yan wasan da za su fafata a gasar Nahiyar Afrika da za a yi nan gaba na ‘yan kasa da shekara 15 da kuma na ‘yan kasa da shekara 19.

Malam Muhammad Bako wanda Ma’aikaci ne a Ma’aikatar Kula da Wasanni da ke Babban Birnin Tarayya kuma Shugaban wadanda za su horar da zakarun da suka fafata a rukunoni daban-daban da suka fito daga Jihohin Kwara da Yobe da Bauchi da Neja da kuma babban birnin tarayya Abuja daga cikin ‘yan wasa maza da mata 103 da suka fafata a gasar da aka share yini 4 gudanarwa.
Malam Muhammad Bako wanda ya bayyana gamsuwarsa ganin yadda matasan da suka fafata a gasar suka nuna dabi’u nagari ya ce Hukumar Kula Da Wasan Badminton Ta kasa za ta karkasa wadannan zakarun ta yadda za a samu saukin kiransu tare da gabatar da su a gasannin da ake sa ran fafatawa da wasu kasashen a Nahiyar Afrika da wasu gasannin da ake sa ran Nijeriya ta amsa kira ba tare da bata lokaci ba
Mai Horar da ‘Yan Wasan ya bayyana kwarin gwiwar cewa wasan na Badminton zai tserewa wasan kwallon kafa ganin cewa a duk manyan gasannin da aka je domin fafatawa irin su Olamfik, da na kasashe renon Ingila wato na Common Wealth duk darajar gwala-kwalen da na azurfa da kuma na tagulla iri daya ne. Misali a shekarar da Najeriya ta ciwo gwal a gasar Olamfik da aka yi a Atlanta,’yan wasan kwallon kafa suna da yawa,darajar gwal da suka ciwo daya ce da wadda Chioma Ajunwa ta lashe a gasar tsalle-tsalle. Wadannan su suka sa yawan gwala-gwalen suka zama biyu baki daya.
Ya sanar cewa yanzu haka kamfanin da ya taimaka aka shirya wannan gasar wato ASHAWAY da ke Singapore ya jaddada cigaba da bayar da goyon bayan da suke bukata domin cigaba da shirya wasanni a matakai daban-daban wadanda za su kara wa wasan kwarjini musamman a kananan makarantu da zai cusa wa dalibai masu kananan shekaru sha’awar wasan.
A karshe ya nemi Gwamnatocin Jihohi da na Tarayya da su samar da isassun filayen wasannin da ba na kwallon kafa ba kadai,Ya koka cewa akasarin gwamnatocin kasar nan sun fi karkata hankulansu ne ga kula da wasan kwallon kafa.Ya nemi su yi koyi da Shugaban Kwalejin Horar Da Malamai Ta Jihar Neja Farfesa Faruk Haruna Rasheed wanda ya samar da filayen wasanni masu inganci da za a iya gudanar da wasannin kasa da kasa ba tare da wata matsala ba,don kayan da aka samar irin na zamani ne musamman wadanda suka gani a filin wasan Badminton.

’Yan sanda sun kashe ’yan fashi 3 a Binuwai

Mahara sun sace bsarake, sun harbi matarsa a ƙauyen Ondo

Sarkin Musulmi ya umarci a fara neman jinjirin watan Muharram

An tsinci gawar wata mata babu kai a Abuja