An yi gobara a Hukumar NFF

A shekaranjiya Laraba ne da tsakar rana gobara ta tashi a Hukumar kula da&nbsp kwallon kafa ta kasa watau NFF.Mai magana da yawun hukumar Mista Ademola Olajire ya shaida wa manema labarai cewa ya samu labarin gobarar ce jim kadan da isarsa ofis don fara aiki a&nbsp inda ya hango hayaki ya murtuke hawa na […]

An yi gobara a Hukumar NFF
An yi gobara a Hukumar NFF

A shekaranjiya Laraba ne da tsakar rana gobara ta tashi a Hukumar kula da&nbsp kwallon kafa ta kasa watau NFF.
Mai magana da yawun hukumar Mista Ademola Olajire ya shaida wa manema labarai cewa ya samu labarin gobarar ce jim kadan da isarsa ofis don fara aiki a&nbsp inda ya hango hayaki ya murtuke hawa na uku.
Sai dai ya zuwa lokacin da muke hada wannan rahoto ba a tabbatar da abin da ya haddasa tashin gobar ba.
Bayanin da Aminiya ta kalato ya nuna gobarar ba ta shafi ofisoshin Shugaban Hukumar da na Sakatare da kuma na bangaren ajiye kudi (accounts) ba saboda yada jami’an kashe gobara suka yi kokarin hana wutar mamaye ofisoshin.
Hukumar NFF dai tana da ofishi ne a Unguwar Wuse Zone 7 da ke Abuja&nbsp