An yi gobara a kasuwar ‘yan Katako ta Kano

A safiyar yau Laraba gobara ta ci akalla shago 22 a kasuwar ‘yan Katako a Rijiyar Lemo da ke Jihar Kano. Jami’in Hulda da Jama’a na Hukumar kashe gobara ta Kano, Alhaji Sa’idu Mohammed ya sanar da manema labarai cewa gobarar ta auko ne da misalin karfe 3 da minti 10 na safiya “Wani mai […]

An yi gobara a kasuwar ‘yan Katako ta Kano

A safiyar yau Laraba gobara ta ci akalla shago 22 a kasuwar ‘yan Katako a Rijiyar Lemo da ke Jihar Kano.

Jami’in Hulda da Jama’a na Hukumar kashe gobara ta Kano, Alhaji Sa’idu Mohammed ya sanar da manema labarai cewa gobarar ta auko ne da misalin karfe 3 da minti 10 na safiya

“Wani mai suna Mohammed Yahaya ne ya kira mu daga Kurna cewa ana gobara a kasuwar da misalin karfe 3 da minti 10 na safe.

“Bayan mun samu labarin gobarar, sai muka tura jami’anmu da motar kashe gobara da misalin karfe 3 da minti 14 domin kashe wutar.”