An yi gumurzu tsakanin ’yan Boko Haram da ’yan banga a Yobe
An yi gumurzu a tsakanin ’yan banga da ’yan Boko Haram a kauyen Yadin Kukuwaa karamar Hukumar Gujba a Jihar Yobe, inda aka hallaka ’yan Boko Haram shida da mutanen kauyen 13 tare da jikkata mutum uku.Wani mazaunin kauyen da ya nemi a sakaye sunansa ya bayyana wa Aminiya cewa, maharan kimanin su 32 a […]
An yi gumurzu a tsakanin ’yan banga da ’yan Boko Haram a kauyen Yadin Kukuwa
a karamar Hukumar Gujba a Jihar Yobe, inda aka hallaka ’yan Boko Haram shida da mutanen kauyen 13 tare da jikkata mutum uku.
Wani mazaunin kauyen da ya nemi a sakaye sunansa ya bayyana wa Aminiya cewa, maharan kimanin su 32 a kan babura sun shiga kauyen da misalin karfe 10 na dare da zimmar daukar fansar mambobinsu biyu da ’yan bangar garin suka kashe a kwanakin baya, inda suka sake haduwa da turhiyar ’yan bangar.
Ya ce lokacinda ake fafatawa akasarin mutanen kauyen sun gudu zuwa wajen gari don yayin da wasu daga cikin ’yan Boko Haram din suka rika bi suna kone gidaje da kashe jama’a, wanda hakan ne ya sa ’yan banga suka janye don kada abin ya munana.
Wani daga cikin mutanen da suka sha da kyar da ya ki amincewa a fadi sunansa ya bayyana wa Aminiya a Damaturu cewa, tun ranar da ’yan bangar da ke gadin kauyensu suka kashe ’yan Boko Hara biyu, ya sha jinin jikinsa cewa da wuya in ’yan uwansu ba su kawo harin ramuwar gayya ba.
Ya ce abin bakin ciki maharan sun kashe musu mutanensu 13 tare da kona musu gidaje.
Duk kokarin da Aminiya ta yi don jin ta bakin Kakakin Rundunar ’Yan sandan Jihar, ASP G. Toyin ya ci tura, amma kansilan yankin Alhaji Nuhu Baba Ambiya ya tabbatar wa Aminiya cewa an kashe ’yan bindigar biyar, su kuma ’yan bindigar sun hallaka mutanen kauyen 10 tare da jikkata mutum uku da kone gidaje da shaguna da dama.