An yi gwanjon rago mafi tsada a duniya

An yi gwanjon dan tinkiya mafi tsada a duniya, aka kuma sayar da shi a kan zunzurutun kudi Yuro 367,500 kwatankwacin dalar  Amurka 490,000. Kudin da yawansu ya kai Naira miliyan 188 da dubu 738 da Naira 200. Dan tunkiyar mai suna ‘Double Dimond’, wanda zuwa yanzu shi ne mafi tsada a duniya, na da […]

An yi gwanjon rago mafi tsada a duniya

An yi gwanjon dan tinkiya mafi tsada a duniya, aka kuma sayar da shi a kan zunzurutun kudi Yuro 367,500 kwatankwacin dalar  Amurka 490,000.

Kudin da yawansu ya kai Naira miliyan 188 da dubu 738 da Naira 200.

Dan tunkiyar mai suna ‘Double Dimond’, wanda zuwa yanzu shi ne mafi tsada a duniya, na da cikar usuli na jinsin tumakin Texel masu daraja da suka samo asali daga yankin Island na kasar Netherlands.

Cikar dan tunkiyar ta hadar da kyan fasalinsa da kyan fuskarsa da launin gashin jikinsa mai ruwan zinariya sai cikar yawan naman jikinsa.

Manoma uku ne suka yi nasarar sayen dan tunkiyar mai wata shida a duniya bayan da aka baje kolinsa a ranar Alhamis 26 ga watan Agustan 2020.

Daya daga cikin mutum ukun da suka yi nasarar mallakar sa, Jeff Aiken ya shaida wa kafar yada labarai ta Sky News cewa ‘Double Diamond’ na da cikar kamala.

“Yana da kyan fasali matuka tun daga launin idanunsa, zuwa launin gashin jikinsa da fasalin kafafunsa da fuskarsa sun tabbatar da cikar kamalarsa.

“Dabba ce mai cikar fasali kuma abin da ake bukata ke nan a jinsi na dabba”, inji manomin.

Da fari an taya dan tunkiyar a kan Dalar Amurka dubu goma, kafin daga bisani farashin ya haura saboda yawan masu bukatar sayen sa.

Yanzu Double Diamond shi ne mafi tsada a duniya bayan da kudinsa ya haura na dan tunkiya mafi tsada da aka yi gwanjonsa a kan Yuro 230,000 a shekarar 2019.

A cewar Jeff Aiken, za a yi bulaguro da dan tinkiyar zuwa garken dabobbi daban-daban domin ya sadu da tumaki da dama ta yadda za a samar da irinshi.

Ya kara da cewa fatarsu shi ne dan tunkiyar mai wata shida ya yi tsawon rai ta yadda za a mai da kudinsa a kuma ci riba.