An yi Hawan Sallah a karon farko cikin shekara hudu a Maiduguri

A karon farko cikin shekara hudu, mahaya dawakai sun gudanar da Hawan Sallah a garin Maiduguri bayan da hare-haren Boko Haram ya hana hakan a baya.Bikin wanda hakimai da masu rike da sarautun gargajiya a karkashin jagorancin Shehun Borno ke hawa dawaki cikin kayan kawa, kan mayar da Maiduguri wata cibiyar yawon bude ido a […]

An yi Hawan Sallah a karon farko cikin shekara hudu a Maiduguri

Yan bindiga suna nuna gwanintarsu a Hawan Sallah a ZariyaA karon farko cikin shekara hudu, mahaya dawakai sun gudanar da Hawan Sallah a garin Maiduguri bayan da hare-haren Boko Haram ya hana hakan a baya.
Bikin wanda hakimai da masu rike da sarautun gargajiya a karkashin jagorancin Shehun Borno ke hawa dawaki cikin kayan kawa, kan mayar da Maiduguri wata cibiyar yawon bude ido a irin wannan lokaci.
Sai dai tun shekarar 2008 aka jingine Hawan Sallah a birnin sakamakon tashin hankalin da ya ki ci ya ki cinyewa wanda ya jawo mutuwar dubban mutane.
Shi kansa Shehun Borno Alhaji Abubakar Garbai Ibn El-Kanemi wani dan kunar bakin wake ya kai masa hari a lokacin Sallar Juma’a a bara, amma ya tsallake ba tare da ko rauni ba, sai dai mutum hudu sun rasu a yayin harin.
Dubban mutane da suka kaurace wa birnin zuwa wasu sassan kasar nan saboda tashin hankalin, an ce sun dawo gida da iyalansu inda suka halarci Sallar Idi karama.
Hawan Sallar yazo ne saboda fara dawowar zaman lafiya a jihar sakamakon sanya dokar ta-baci da kuma bayyanar matasa ’yan banga da ke farautar ’yan Boko Haram da ’yan bangar JTF.
dimbin hakimai da dagatai da masu rike da sarautun gargajiya ne suka yi hawa a gaban fadar Shehun Borno, inda dubban jama’a daga ciki da wajen Maiduguri suka taru don kashe kwarkwatar ido.
dimbin jama’a ne suka fita masallatan Idi da ke garin Maiduguri, yayin da Gwamnan Jihar Borno, Kashim Shettima da Shehun Borno Abubakar Garbai da suka yi Sallah a Dandalin Ramat, suka nuna godiya ga Allah kan dawowar zaman lafiya a jihar.
Shettima wanda ya halarci Hawan Sallar ya yaba wa mutanen birnin da suka dawo gidajensu da shagunansu a yankunan da rikicin ya shafa.
Da yamma Gwamna Shettima ya shirya walimar cin abincin rana a gidan gwamnati inda ya yaba wa rundunar JTF da ’yan bangar JTF kan kokarinsu na dawo da zaman lafiya, wadda ta jawo aka gudanar da Sallar Idi cikin kwanciyar hankali.
Ya ce, “Abin bakin ciki ne yadda aka halaka daruruwan mutanen jihar, aka salwantar da dukiya ta miliyoyin Naira ciki har da ajujuwan makarantun sakandare da firamare 800 da aka lalata a sassan jihar.”
Shetiima ya ce sadaukar da kai na JTF da ’yan bangar JTF da mutanen jihar masu kishi ne ya sa Borno take samun zaman lafiya.
Gwamnan ya yi alkawarin ci gaba da ba jami’an tsaro goyon baya a yakin da suke yi da ’yan ta’adda. “Mu a matsayin gwamnati ba za mu manta da kokarin JTF da ’yan bangar JTF da kafofin watsa labarai da daukacin al’ummar Jihar Borno masoya zaman lafiya kan dimbin goyon baya da addu’o’i da damuwar da suka nuna kan yadda za a kawo karshen ayyukan ta’addanci a jiharmu da kuma kasar nan baki daya,” inji shi.
Ya ce, “Yunkurin dukkan bangarori da goyon bayan da muka samu daga dukkan bangarorin jama’a ne ya sa aka samu nasarar gudanar da bukukuwan karamar Sallah lafiya, kuma muna kira ga kowa da kowa a ci gaba da addu’o’in tabbatar zaman lafiya a jiharmu da kasarmu.”

…Hawan Sallah ya dawo a Zariya bayan shekara biyu

Daga Aliyu Babankarfi, Zariya

Kasancewar zaman lafiya da kwanciyar hankali ya samu a Jihar Kaduna, Hawan Sallah da aka saba a kasar Hausa da masarautar Zazzau ta shekara biyu ba ta yi ba ya gudana cikin kwanciyar hankali da nishadi a bana.
Wakilinmu ya rawaito cewa karamar Sallah a masarautan Zazzau ta bana ta bambanta da bara, domin duk da rashin kudi da walwala da ke damun wasu sassan Arewa, al’ummar Zariya sun yi Sallar cikin nashadi.
Rahotanni sun tabbatar da cewa baki daga sassa daban-daban da suka hada da makwabtan Najeriya sun taho Zariya don halartar bikin karamar Sallar.
Mai martaba Sarkin Zazzau Alhaji Shehu Idris ya nuna farin cikinsa ga al’ummar masarautar ta hanyar yin hawan da aka dade ba a yi irinta ba, dauke da tawagar hakimai sama da 100.
Aminiya ta gano bakin da suka ziyarci Zariya sun koma gida cikin farin ciki suna nuna jin dadi kan irin tsarin da suka gani a Hawan Sallah na masarautar Zazzau a bana.
A jawabin Mai martaba Sarkin Zazzau Alhaji Shehu Idris ya yaba wa al’ummarsa ne inda ya ce, “Kamar yadda muka saba a kowace shekara a rana irin ta yau, mukan yi wa jama’ar kasar Zazzau jawabi a kan muhimman abubuwan da suka shafi ci gabanmu tare da kawo mana zaman lafiya. Ina kara yi wa Mai girma Gwamnan Jihar Kaduna Alhaji Mukthar Ramalan Yero da dukkan jami’an tsaro godiya saboda kokarin da suke yi dare da rana wajen tabbatar da zaman lafiya a Jihar Kaduna. Haka kuma ina isar da godiya kwarai ga jama’ar kasar Zazzau saboda hadin kai da suke bayarwa wajen tabbatar da zaman lafiya birane da kauyuka.”
Ya kara da cewa,    “Kamar yadda muka sani cewa ci gaba kowane iri, ba ya samuwa sai da zaman lafiya, saboda haka ina kara jawo hankalin jama’armu su ci gaba da tattalin zaman lafiya, a guji yada jita-jita, a ci gaba da ba jami’an tsaro cikakken hadin a kokarin da suke yi na kawar da miyagun laifuffuka da suka damu kasarmu. Ina son jama’ar birane da kauyuka mu ci gaba da addu’a Allah Ya kara tabbatar wa Jihar Kaduna da kasarmu cikakken zama lafiya.”
Mai martaba Sakin ya ci gaba da cewa, “Ina son in dauki wannan dama in yi godiya ta musamman ga malaman da suka gabatar da Tafsirin Alkur’ani Mai girma a waan azumin Ramadan saboda cikakkiyar nasara da aka samu wajen gabatar da tafsirin. Nasarar ta samu ne saboda gabatar da tafsirin da malaman suka yi ba tare da bata wani ko sukar juna ba, sai dai fadin gaskiya tsakaninsu da Allah, wannnan abin farin ciki ne, Allah Ya kara hada kan Musulmi a ko’ina muke.
Sarkin kuma ya jawon hankalin jama’a su rika sa ido game da bakin da suke shigowa garuruwansu. Haka kuma su rika tabbatar da sahihancin bakin kafin su ba su masauki ko hayar gidaje ko sauke su a oel-otel.
Sai ya ce, “Ina kara kira ga jama’armu su kara sa ido don sanin irin halin da ’ya’yanmu suke ciki, gudun kada batagari su gurbata mana su, ta amfani da su wajen aikata miyagun laifuffuka sa sanya su shaye-shaye da sace-sace da sauransu. Iyaye su matsa wa ’ya’yansu su koyi sana’a idan aikin ofis ko kwangila ba su samu ba.”