An yi jana’izar Bello Maitama a Kano

An birne shi a makabartar Tarauni da ke Kano

An yi jana’izar Bello Maitama a Kano

Bello Maitama

An gudanar da jana’izar tsohon Ministan Harkokin Cikin Gida na Najeriya kuma Sardaunan Dutse, Alhaji Bello Maitama Yusuf, a Fadar Sarkin Kano da yammacin Juma’a.

Marigayin dai ya rasu ne yana da shekara 76 a duniya, bayan gajeruwar jinya.

Ya rasu ya bar mata biyu da ƴaƴa 10; maza biyar, mata biyar.

Marigayin dai ƙwararran lauya ne wanda ya yi Minista a jamhuriya ta biyu kuma ya zama Sanata a jamhuriya ta huɗu.

An birne shi ne a makabatar Tarauni da ke birnin Kano kamar yadda Addinin Musulunci ya tanadar.

Ga wasu daga cikin hotunan jana’izar tasa:

 

Manyan alhinin Najeriya a 2024

’Yan sanda sun kama waɗanda suka shirya rikicin ‘yan daba a Kano

Ɗan Gwamnan Jigawa ya rasu kwana guda bayan rasuwar mahaifiyarsa

Mutum 38 ne suka mutu a haɗarin jirgin sama a Kazakhstan