An yi jana’izar daliban Kano 8 da suka rasu a hadarin mota

A safiyar jiya Alhamis ne aka yi jana’izar daliban sakandare takwas da suka rasu a hadarin mota a Ibadan ta Jihar Oyo.daliban takwas da direbansu sun yi hadari ne a ranar Talata da daddare lokacin da suke dawowa daga Legas inda suka wakilci Jihar Kano a wajen gasar da aka shirya wa Makarantun Sakandaren Kimiyya […]

An yi jana’izar daliban Kano 8 da suka rasu a hadarin mota
An yi jana’izar daliban Kano 8 da suka rasu a hadarin mota

A safiyar jiya Alhamis ne aka yi jana’izar daliban sakandare takwas da suka rasu a hadarin mota a Ibadan ta Jihar Oyo.
daliban takwas da direbansu sun yi hadari ne a ranar Talata da daddare lokacin da suke dawowa daga Legas inda suka wakilci Jihar Kano a wajen gasar da aka shirya wa Makarantun Sakandaren Kimiyya na kasa, inda wata majiya ta ce tayar motarsu mai dauke dalibai 12 ce ta fashe, inda motar ta kwace daga direban ta yi hadari daliban takwas da direban suka rasu, yayin da sauran dalibai uku suka samu raunuka akwa kwantar da su a wani asibiti a Jihar Oyo, kafin a iso da gawarwaki da wadanda suka tsira daga hadari zuwa Kano da yammacin ranar Laraba.
Dubban Musulmi ciki har da Gwamnan Jihar Kano Dokta Abdullahi Umar Ganduje da kwamishinoni da mukarrabansa da wakilan Masarautar Kano da iyayen daliban das aura jama’a ne suka halarci Sallar Jana’izar wadda aka yi a kofar Fadar Mai martaba Sarkin Kano a karkashin jagorancin Babban Limamin Kano Farfesa Sani Zahraddeen.
Gwamna Abdullahi Ganduje wanda ya gana da iyayen daliban da ’yan uwansu a gidan gwamnati gabanin kawo gawarwakinsu, har ila yau shi ne ya karbi gawarwakin lokacin da aka kawo su ta jirgin sama a filin jirgin sama na Malam Aminu Kano a yammacin shekaranjiya Laraba.
Gwamnan Jihar Oyo Alhaji Isiak Abiola Ajimobi da hadarin ya auku a jiharsa ya aike da sakon ta’aziyya ga Gwamna Abdullahi Ganduje. Gwamnan ya mika wannan ta’aziyya ce a lokacin da ya ziyarci dalibai takwas da suka tsira da ransu a dakin kula da ’yan hadari na Asibitin Koyarwa na Jami’ar Ibadan (UCH), inda ya yi alkawarin daukar nauyin jinyarsu har zuwa lokacin da za a sallame su daga asibitin.