An yi jana’izar hafsan soja da aka sace a Kaduna

An yi jana’izar hafsan sojan nan da aka sace a Kaduna Kanar Sama’ila Inusa a shekaranjiya Laraba bayan da aka tsinci gawarsa a ranar Talata. An binne marigayin ne  a makabartar tsohuwar Kwalejin Horar da kananan Hafsoshin Soji (NDA) da ke Kaduna bayan yi masa Sallar Janaza kamar yadda addinin Musulunci ya tanada.An haifi marigayin […]

An yi jana’izar hafsan soja da aka sace a Kaduna
An yi jana’izar hafsan soja da aka sace a Kaduna

An yi jana’izar hafsan sojan nan da aka sace a Kaduna Kanar Sama’ila Inusa a shekaranjiya Laraba bayan da aka tsinci gawarsa a ranar Talata. An binne marigayin ne  a makabartar tsohuwar Kwalejin Horar da kananan Hafsoshin Soji (NDA) da ke Kaduna bayan yi masa Sallar Janaza kamar yadda addinin Musulunci ya tanada.
An haifi marigayin ne a karamar Hukumar Nasarawa da ke Jihar Kano a 1972, kuma ya hakarci makarantu daban-daban inda ya shiga Kwalejin NDA a 1992 ya kammala digirinsa na farko a kimiyyar halittu a 1997. Ya yi aiki a wurare da dama a fannin soja inda a bara aka kara masa girma zuwa Kanar.
Rundunar Sojin Najeriya ta fadi a ranar Talata cewa an gano gawar Kanar Sama’ila a kusa da kauyen Ajyaita da ke kan titin zagaye na gabashin Kaduna.
Wasu ’yan bindiga da ba a san ko su wane ne ba suka sace Kanar Sama’ila a lokacin da yake cikin motarsa tare da matarsa a kan hanyar Kamazo da ke kudancin birnin Kaduna. ’Yan bindigan sun sauke matar nan take sannan suka yi hanyar Abuja da mijinta kafin daga bisani aka tsinci gawarsa.
Rundunar Sojin a lokacin da aka sace jami’in ta fitar da sanarwa inda ta yi alkawarin bayar da ladar Naira miliyan daya ga duk wanda ya ba ta bayanin da zai taimaka wajen gano Kanar Sama’ila.
Wata sanarwa dauke da sa hannun Kakakin Rundunar ta kasa, Kanar Sani Kukasheka Usman ta ce binciken da aka kaddamar an fahimci cewa ga dukkan alamu ’yan bindigan sun kashe marigayi Samaila ne tun a ranar da suka sace shi. “Saboda a lokacin da aka gano gawarsa har ta soma rubewa a kauyen  Aiyaita da ke kudancin birnin Kaduna. Rundunar Sojan Najeriya na bakin cikin sanar da jama’a cewa an tsinci gawar Kanar Sama’ila Inusa wanda aka sace shi a ranar Lahadi 27 ga Maris, a yau (Talata) da misalin karfe  6.00 na yamma. Muna sanar da cewa ko shakka babu duk wanda ke da hannu wajen sacewa da kashe shi za mu gano su domin su fuskacin hukunci,” inji shi.