…An yi jana’izar kwamishinan yada labarai
A ranar Litinin Allah Ya yi wa kwamishinan yada labarai na Jihar Kebbi, Alhaji Sani Mohammed Kangiwa rasuwa, bayan wata doguwar rashin lafiya da ya yi. Kafin rasuwarsa, marigayin ya taba rike mukamin sakataren yada labarai na gwamnan jihar ta Kebbi, a lokacin mulkin soja. Ya kuma taba zama shugaban karamar Hukumar Arewa-Dandi, daga nan […]

A ranar Litinin Allah Ya yi wa kwamishinan yada labarai na Jihar Kebbi, Alhaji Sani Mohammed Kangiwa rasuwa, bayan wata doguwar rashin lafiya da ya yi.
Kafin rasuwarsa, marigayin ya taba rike mukamin sakataren yada labarai na gwamnan jihar ta Kebbi, a lokacin mulkin soja. Ya kuma taba zama shugaban karamar Hukumar Arewa-Dandi, daga nan ya zama kwamishinan yada labarai.
Ya rasu yana da shekaru hamsin da hudu kuma ya bar matan aure ukku da ’ya’ya goma sha bakwai.
Daga cikin wadanda suka sami halartar jana’izar har da Gwamna Alhaji Sa’idu dakingari da wasu daga cikin jami’an gwamnatinsa.