An yi jana”izar Lawal Kaita a Katsina
Tsohon gwamnan tsohuwar jihar Kaduna, Alhaji Lawal Kaita wanda ya rasu a yammacin ranar Talatar da ta gabata, an binne shi a makabartar Danmarina da ke Katsina bayan an yi masa sallar jana’iza a fadar Sarkin Katsina. Wadanda suka halarci jana’izar sun hada da manyan jami’an gwamnati da sarakunan gargajiya da ’yan kasuwa da […]

Tsohon gwamnan tsohuwar jihar Kaduna, Alhaji Lawal Kaita wanda ya rasu a yammacin ranar Talatar da ta gabata, an binne shi a makabartar Danmarina da ke Katsina bayan an yi masa sallar jana’iza a fadar Sarkin Katsina.
Wadanda suka halarci jana’izar sun hada da manyan jami’an gwamnati da sarakunan gargajiya da ’yan kasuwa da ’yan siyasa da kuma manyan jami’an tsaro.
Tawagar Gwamnatin Tarayya karkashin jagorancin Ministan Sufurin jiragen Sama, Hadi Sirika, sun hada da Ministan Tsaro, Mansur Dan-Ali da Ministan Albarkatun Ruwan sha, Sulaiman Adamu Kazaure da Ministan Shari’a Abubakar Malami da Babban Mai Taimaka wa Shugaban Kasa Kan Harkokin Yada Labarai, Garba Shehu da kuma Sakataren Dindindin na Ma’aikatar Sadarwa, Abdul’aziz Mashi.