An yi jana’izar mutum 34 da Boko Haram ta kashe a Yobe

Mayaƙan sun kashe da dama tare da raunata wasu.

An yi jana’izar mutum 34 da Boko Haram ta kashe a Yobe

Aƙalla mutum 34 da ‘yan ta’addan Boko Haram suka kashe aka yi wa jana’iza a garin Babbangida da ke ƙaramar hukumar Tarmuwa a Jihar Yobe.

Jana’izar ta samu jagorancin Gwamnan Jihar, Mai Mala Buni wanda mataimakinsa, Alhaji Idi Barde Gubana, ya wakilta da kuma wasu jami’an gwamnatin Jihar.

Babban limamin cibiyar kula da addinin Musulunci da babban Masallacin Juma’a na Damaturu, Ustaz Hudu Muhammad ne, ya gabatar da sallar jana’izar mamatan.

An yi jana’izar mamatan ne a kofar Mai Martaba Mai Jajere da ke garin Babbangida.

Amma wata majiyar da ke garin Mafa ta tabbatarwa Aminiya cewar adadin mutanen da ‘yan ta’addan suka hallaka ya zarce 80.

Majiyar ta ce tuni ‘yan uwan wasu da suka rasu suka kwashe su domin yi musu sutura kamar yadda addinin Musulunci ya tanadar.

Da yake jawabi, mataimakin gwamnan jihar, Alhaji Idi Barde Gubana, ya nuna alhinin gwamnatin jihar game da kisan.

Ya yi addu’ar Allah ya musu sakayya da gidan Aljannatul Firdausi.

Gwamnatin jihar ta bayar da tallafin Naira Mlmiliyan 30 ga iyalan mamatan da kuma waɗanda suka jikkata.

Kazalika, ta umarci Hukumar Bayar da Agajin Gaggawa ta Jihar (SEMA), da ta kai wa wadanda lamarin ya shafa tallafin kayan abinci.

Ya kuma bayar da tabbacin cewar gwamnatin za ta haɗa kai da jami’an tsaro don ganin an zakulo ‘yan ta’addan da suka aikata kisan.

Gwamnan, ya nemi al’umma da su ci gaba da addu’ar neman zaman lafiya ga jihar da ma ƙasa baki ɗaya.

NLC ta yi watsi da ƙara kuɗin kiran waya da data

DSS ta gurfanar da Mahdi Shehu kan zargin ta’addanci

Sojoji sun kashe mataimakin Bello Turji

Harin ’Yan Fashi: Buni ya jajanta wa ’yan kasuwar Ngalda