Yadda aka yi Jana’izar Sarkin Gobir ba tare da gawarsa ba

An gudanar da Sallar Jana’iza ba tare da gawa ba a fadar Sarki Isa Muhammad Bawa

Yadda aka yi Jana’izar Sarkin Gobir ba tare da gawarsa ba

Masarautar Gobir ta gudanar da Sallar Jana’iza ga Sarki Isa Muhammad Bawa ba tare da gawarsa ba, sakamakon kisan gilla da ’yan bindiga su yi masa.

Dan basaraken da aka sace su tare amma suka sako shi a daren Laraba ya ce ’yan bindigar sun binne gawar mahaifin nasa da suka kashe a ranar Talata.

Dubban jama’a ne suka halarci sallar sarkin da kwanansa ya kare bayan ya shafe kusan kwanaki 26 a hannun ’yan bindiga

Hotunan yadda aka yi Sallar Jana’izar Sarkin Gobir ba tare da gawarsa ba (Salatul Ga’ib) bayan samun labarin cewa ’yan bindiga sun binne gawarsa.

Babban dan marigayin kuma Turakin Gobir, Surajo Isa, ya shaida wa Aminiya cewa da misalin karfe 10 na safiyar Alhamis aka gudanar da Sallar, wadda Babban Limamin Sabon Birni, Imam Dahiru, ya jagoranta.

“Alhamdulillah game da rayuwar Sarki, muna alfahari da shi domin ya gudanr da rayuwarsa ne wajen hidimta wa al’ummarsa,” in ji shi.

Surajo ya bayyana godiya ga al’umma bisa yadda suka nuna musu kauna da tausayawa a wannan yanayi da kuma lokacin da aka sace sarkin.

Alhaji Isa ya rasu ya bar mata uku da yaya 18 da kuma jikoki.

Davido zai bai wa marayu tallafin N300m a Najeriya

Ba mu yanke hukunci kan ƙudirin harajin Tinubu ba — Abbas

Masu garkuwa da mutane na neman N10m kan manoma 6 a Taraba

Hotunan Gobarar Kasuwar Laranto da ke Jos