An yi jana’izar Shehun Dikwa
Karfe 10 na safiyar Lahadi 24 ga Janairu 2021 za a yi Sallahar Jana’izar Shehun Dikwa
Da misalin karfe 10 na safiyar Lahadi, 24 ga Janairu, 2021 aka yi Sallar Jana’izar Shehun Dikwa, Alhaji Mohammed Ibn Masta II El-Kanemi.
Shehun Dikwa ya rasu ne a Abuja, inda ake jinyar sa sakamakon rashin lafiyar da ya dade yana fama da shi. Ya rasu a ranar Jum’a, kwana guda bayan an kai shi Abuja domin jinya.
- An yi garkuwa da shugaban ’yan bindiga
- Tashirn farashin awara ya jawo ce-ce-ku-ce a Kano
- Yadda Kwamandojin ’yan bindiga suka tuba a hannun Dokta Gumi
Tun da farko an shirya gudanar da jana’izar Sarkin Dikwa, Alhaji Mohammed Ibn Masta II El-Kanemi da misalin karfe biyar na yammacin ranar Asabar, amma daga bisani aka dage zuwa karfe 10 na safiyar Lahadi.
Sakaren Gwamnatin Jihar Borno, Alhaji Usman Jidda Shuwa ne ya sanar rasuar tasa garin Biu, jim kadan bayan Gwamna Babagana Umara Zulum ya mika wa sabon Sarkin Biu, Alhaji Mai Mustapha Umar Mustapha sandar mulki.
Karo na uku ke nan da manyan sarakunan Jihar Borno suke mutuwa a lokacin da babu tazara a tsakani, ciki har da Shehun Bama da Sarkin Biu wadanda suka rasu a shekarar 2020.
Margiyayin ya zama Shehun Dikwa ne a shekarar 2010 bayan an kafa Masarautar Bama, wadda a lokacin ita ce Hedikwatar Masarutar ta Dikwa.
Mamacin wanda ya rasu yana da shekaru 70, ya yi karatunsa na firamare ne a makarantar Central Primary School, da ke garin Bama.
Daga baya ya je kwalejin horas da malamai ta Mubi Teachers’ College, inda ya samu shaidar koyarwa ta Grade III a 1961.
Shugaba Buhari ya mika ta’aziyyarsa ta bakin kakakinsa, Garba Shehu ga Gwamnatin Jihar Borno, al’ummar Jihar da kuma Masarautar.
Buhari ya bayyana mamacin a matsayin dattijo wanda ya sadaukar da rasuyarwa domin amfanar al’ummarsa.
“Marigayi Shehun Dikwa ya ba da muhimmiyar gudunmuwa wajen samar da hadin kai da zaman lafiya a kasa baki daya, kuma za a yi matukar kewarsa.
“Basaraken ya rasu a lokacin da kasar ke matukar bukatar irin gudunmuwarsa.
“Allah Ya gafarta masa, Ya kuma yi masa sakayya da Aljannah. Su kuma iyalai, Allah Ya ba su hakurin jure wannan babban rashi,’’ inji Buhari a ta’aziyyarsa ga Shehun Borno, Abubakar Ibn Umar Garbai El-Kanemi, Buhari ya ce.