An yi jana’izar tsohon Limamin Masallacin Harami, Sheikh Al-Sabuni
Sheikh Al Sabuni ya rasu bayan shafe shekara 91 a doron kasa.
An yi jana’izar babban Malami kuma tsohon Limamin Masallacin Harami na Makkah, Sheikh Muhammad Ali Al-Sabuni a kasar Turkiyya.
Sheikh Muhammad Ali Al-Sabuni, na daga cikin limaman sallar Taraweeh a Masallacin Harami a wata Ramadan kimanin shekara 57 da suka gabata.
- Fuskokin Limaman Sallar Tarawih da Tahajjud a Makkah
- Gobara ta babbake unguwar marasa galihu a Saliyo
- Coronavirus ta kashe mutum 300,000 a Brazil
Sheikh Al-Sabuni ya rasu ne a garin Yelwa na kasar Turkiyya bayan shafe shekara 91 a doron kasa, a ranar Juma’a, 6 ga watan Sha’aban 1442 Hijiriyya.
An haifi Sheikh Al-Sabuni ne a kasar Syria, kuma ya rubuta litittafai da dama kan ilimin tafsirin Al-Kur’ani mai girma, ciki har da “Taisiru Karimur Rahman Fi Tafsiri Kalamul Mannan,” wanda ya shahara da suna Tafsirin Sabuni.
Marigayin ya shafe kimanin shekara 28 yana koyarwa a Tsangayar Shari’ar Musulunci da ke Jami’ar Ummul Kura da kuma Tsangayar Ilimi da Tarbiyya ta Jami’ar Musulunci ta Sarki Abdul Aziz, dukkansu a birnin Makkah.
A watan Azumin Ramadan lokacin Hijirar Manzon Allah (SAW) daga birnin Makkah zuwa Madina tana shekara ta 1385, Sheikh Muhammad Al-Sabuni ya yi jagorancin Sallar Taraweeh a Masallacin Harami na Makkah.