An yi jana’izar Umaru Dikko a Zariya
A ranar Talata da misalin karfe 2:00 na rana ne aka yi jana’izar tsohon Ministan Sufuri Alhaji Umaru Dikko a fadar Mai martaba Sarkin Zazzau da ke Zariya.Jana’izar wadda Babban Limamin Zazzau Limamin Kona Sheikh Muhammadu Sani Aliyu ya jagoranta, mutane da dama ne daga sassan kasar nan suka halarta, ciki har da Ministan Ayyuka […]

A ranar Talata da misalin karfe 2:00 na rana ne aka yi jana’izar tsohon Ministan Sufuri Alhaji Umaru Dikko a fadar Mai martaba Sarkin Zazzau da ke Zariya.
Jana’izar wadda Babban Limamin Zazzau Limamin Kona Sheikh Muhammadu Sani Aliyu ya jagoranta, mutane da dama ne daga sassan kasar nan suka halarta, ciki har da Ministan Ayyuka na Musamman Kabiru Tanimu Turaki wanda ya jagoranci wakilan Gwamnati Taraya.
Idan ba a mantaba a Talatar makon jiya ne Allah Ya yi wa tsohon Ministan rasuwa yana da shekara 78 a duniya a wani asibiti a birnin Landan.
Marigayi Umaru Dikko ya rasu ya bar matan aure biyu da ’ya’ya 11 da kuma jikoki, kuma za a ci gaba da tuna shi kan irin gudumawar da ya bayar a bangaren siyasa da ci gaban kasa.