An yi Jana’izar Wanda Mahara Suka Harbe A Zariya
An yi sallar jana’izar shugaban mahauta na kasuwar Tudun Wada, Zariya, Mohammed Bashir (Govinda) wanda ’yan bindiga suka harbe har lahira
An gabatar da sallar jana’izar shugaban mahauta na kasuwar Tudun Wada, Zariya, Mohammed Bashir (Govinda) a ranar Laraba, bayan ’yan bindiga suka harbe har lahira.
Dan uwan mamacin, Suleiman Abubakar ya ce Marigayi Bashir an harbe shi ne lokacin da maharan suka kai masu farmaki a garin kasuwar magani da ke Karamar Hukumar Kajuru, jihar Kaduna, ranar talata, a kan hanyarsu ta dawowa daga gona.
’Yan bindigar sun kuma yi awon gaba da mutane hudu a cikin su har da wani malamin Kwalejin Ilmi ta Tarayya da ke Zariya kuma Mai sharhi a kafafen yada labarai, Mallam Sama’ila Sahabi.
Sauran wadanda aka sace akwai kanin shi Sidi Aliyu Sahabi da kuma wadansu mutane guda biyu.
- Tinubu ya naɗa sabuwar Shugabar Ma’aikatan Gwamnatin Tarayya
- Ina roƙon ’yan Nijeriya da su ƙauracewa shiga zanga-zanga — Zulum
Rahotanni na nuni da cewa daga cikin mutum hudun, akwai mutum daya da ya sami tserewa daga hannu maharan.
Aminiya ta gano cewa dukkan wadanda ’yan bindigar suka kama ’yan asalin Tudun Wada, Zariya ne da suke da gona a Kasuwar Magani inda suke zuwa don gudanar da aikin noma.
Mallam Musa Sahabi dan uwan mutane biyu da aka sace, ya ce labarin da suka samu ya nuna kamar cinne aka yi masu.
“Domin kuwa an ce sun same su ne a daki, bayan sun dawo gona. Kuma har suna tambaya ina ne dakin daya daga cikin wadanda suka sace,” in ji shi.
Da wakilinmu ya tuntubi kakakin Rundunar ‘yan sanda ta jihar Kaduna, ASP Mansir Hassan, wayaraa na rufe a lokacin hada wannan labarin.