An yi jarabawar shiga sojan Indiya da dan kamfai

Babbar Kotun Patna ta bukaci ma’aikatar tsaro ta kasar Indiya ta bayyana mata dalilin sayan daruruwan matasa suka tube daga su sai dan kamfai don rubuta jarabawar daukar aikin soja, a gundumar  Muzaffapur da ke Jihar Bihar, a cewar wani lauya.Fiye da mutum dubu da ke neman aikin akawu, aka sa suka tube daga su […]

An yi jarabawar shiga sojan Indiya da dan kamfai
An yi jarabawar shiga sojan Indiya da dan kamfai

Babbar Kotun Patna ta bukaci ma’aikatar tsaro ta kasar Indiya ta bayyana mata dalilin sayan daruruwan matasa suka tube daga su sai dan kamfai don rubuta jarabawar daukar aikin soja, a gundumar  Muzaffapur da ke Jihar Bihar, a cewar wani lauya.
Fiye da mutum dubu da ke neman aikin akawu, aka sa suka tube daga su sai dan kamfai a wajen rubuta jarabawa, don gudun satar amsa.
Bayan kotu ta yi nazarin rahotobn yadda aka gudanar da jarabawar, kamar yadda jaridar Hindi ta ruwaito, sai kawai ta bukaci ma’aikatar tsaro ta yi mata bayani. Kotun dai na shirin zama don buin bahasin lamarin a ranar uku ga watan Afirilu mai zuwa.
Hukumomin sojan kasar, sun bayyana cewa,  da masu rubuta jarrabawar, sukan boye takardu dauke da amsoshin tambayoyi, ko kuma su taho da na’urorin da za su taimake su, sdake a cikin tufafin su.
Masu rubuta jarrabawar sun harde kafa, inda suka yi amfani da cinyarsu a matsayin teburin rubuta jarrabawar da dauke su sa’a guda cur. Duk da cewa wasu sun koka da sanyi da rashin jin dadin zama, amma ba su da zabi.