An yi jerin gwano don la’antar ayyukan fyade a Jihar Adamawa

Mutum fiye da dubu ne da suka kunshi iyayen yara da kuma kungiyoyi masu zaman kansu suka yi jerin gwano don la’antar ayyukan fyade a Jihar Adamawa. Masu jerin gwanon dai sun yi tattaki ne zuwa Hedkwatar ’Yan sanda da Babbar Kotun Jihar da kuma Gidan Gwamnatin Jihar domin nuna rashin jin dadinsu kan yawan […]

An yi jerin gwano don la’antar ayyukan fyade a Jihar Adamawa

Gwamna Umaru Fintiri na Jihar Adamawa

Mutum fiye da dubu ne da suka kunshi iyayen yara da kuma kungiyoyi masu zaman kansu suka yi jerin gwano don la’antar ayyukan fyade a Jihar Adamawa.

Masu jerin gwanon dai sun yi tattaki ne zuwa Hedkwatar ’Yan sanda da Babbar Kotun Jihar da kuma Gidan Gwamnatin Jihar domin nuna rashin jin dadinsu kan yawan aukuwar fyade da ake yi wa yara kanana, sannan masu aikata laifuffukan suke tafiya ba tare da kwakkwaran hukunci ba.

Masu jerin gwanon dauke wasu takardun da suke fadin ‘A kama masu fyade,’ sun ce ya kamata gwamnati ta yi wani tsari da za a rika ilimantar da yara kanana game da illolin fyade idan suka baro gida.

Sun bukaci gwamnati da kotuna su dauki tsauraran matakai game da duk wanda aka kama yana aikata fyade.

Daya daga cikin wadanda suka gudanar da jerin gwanon, kuma shugaban daya daga cikin kungiyoyin da suka shirya tattakin, Yusuf Sunday ya shaida wa Gwamnan Jihar Adamawa Umaru Fintiri cewa iyayen yara da yara na kukan zuci game da yadda wannan abu ya yi tsamari a tsakanin al’ummar Adamawa.

Ya kara da cewa, “Mun fito kwanmu da kwarkwatarmu a yau domin mu kawo maka kukanmu da kuma ’yan jarida domin su taya mu yada wa kasar irin yadda fyade ya yi yawa a Jihar Adamawa.”

Hajiya Asma’u Joda wadda Shugaba ce a wata kungiya da ta shiga jerin gwanon ta roki Gwamna Fintiri ya duba wannan lamarin wajen samo mafita.

A jawabin, Gwamna Umaru Fintiri ya dauki alwashin hukunta duk wanda aka kama da yi wa wata fyade inda ya ce zai yi iya kokarinsa wajen ganin an kama masu irin wadannan ayyuka.

Ya ce hawansa kujerar mulki ya karanta a jaridu an samu matsalolin fyade akalla goma, don haka yana tabbatar wa mutanen kasa da Jihar Adamawa cewa bukaci Babban Joji da Ma’aikatar Shari’a ta Jihar su bi kowace kara da aka yi wadda ta shafi fyade domin ganin an hukunta duk wanda ya aikata laifin.

Davido zai bai wa marayu tallafin N300m a Najeriya

Ba mu yanke hukunci kan ƙudirin harajin Tinubu ba — Abbas

Masu garkuwa da mutane na neman N10m kan manoma 6 a Taraba

Hotunan Gobarar Kasuwar Laranto da ke Jos