An yi karar wani basarake kan miliyan shida a Gusau
Wani Basarake karkarshin masarautar Gusau kuma fitatcen dan siyasa da aka fi sani da Kabiru Isa Liyafa, dan Isan Gusau ya gurfana gaban kotun shari’ar Musulunci da ke Samaru, a karamar Hukumar Gusau, babban birnin Jihar Zamfara.Wata ’yar kasuwa, Hajiya Kyauta Yahaya, ita ce ta kai karar a kotun da mai shari’a Mukhtar Ibrahim ke […]
Wani Basarake karkarshin masarautar Gusau kuma fitatcen dan siyasa da aka fi sani da Kabiru Isa Liyafa, dan Isan Gusau ya gurfana gaban kotun shari’ar Musulunci da ke Samaru, a karamar Hukumar Gusau, babban birnin Jihar Zamfara.
Wata ’yar kasuwa, Hajiya Kyauta Yahaya, ita ce ta kai karar a kotun da mai shari’a Mukhtar Ibrahim ke alkalanci, inda take zarginsa da karbar mata kaya bashi kuma ya dauki tsawon lokaci bai biya ba. Kudin dai su ne, Naira Miliyan shida da dubu dari uku.
Kamar yadda mai karar ta bayyana wa kotu, cikin kayayyakin da ake zargin ya amsa, akwai riguna da kayan mata, wadanda suka kunshi les-les da atamfofi da takalma da ababen wuya da shaddodi da turaruka, da dai sauransu.
Barista Aminu Janaidu, shi ne lauyan wanda ake kara kuma ya kalubalanci koken da aka shigar ga kotun, don haka ya roki kotu da ta umurci lauyan ita mai kara da ya bayyana wa kotu farashin kowane abu da aka amsa da kuma ko guda nawa ne ta bayar, domin kotu ta iya tantance kudin kowanne kayan da kuma yadda huldar ta kasance a tsakaninsu.
Alkali Mukhtar Ibrahim ya daga sauraron karar har zuwa ranar 23 ga wannan wata da muke ciki.