An yi kira ga dillalan mai dangane da matsalar fetur

An yi kira ga ’ya’yan kungiyar masu sayar da man fetur ta kasa (IPMAN) da su gaggauta kawo karshen matsalar man fetur da ake fama da ita a wannan kasar.Mai martaba Sarkin Katsinan Gusau, Alhaji Ibrahim Bello ne ya yi wannan kiran a fadarsa, lokacin da yake karbar bakuncin shugaban kungiyar ta kasa da ya […]

An yi kira ga dillalan mai dangane da matsalar fetur
An yi kira ga dillalan mai dangane da matsalar fetur

An yi kira ga ’ya’yan kungiyar masu sayar da man fetur ta kasa (IPMAN) da su gaggauta kawo karshen matsalar man fetur da ake fama da ita a wannan kasar.
Mai martaba Sarkin Katsinan Gusau, Alhaji Ibrahim Bello ne ya yi wannan kiran a fadarsa, lokacin da yake karbar bakuncin shugaban kungiyar ta kasa da ya ziyarce shi.
Ya kara da cewa ya yi matukar farin ciki da ’ya`yan kungiyar suka ziyarce shi, kuma ya ce a kodawane lokaci kofar fadarsa a bude take don neman shawarwar. Ya kuma nemi ’ya’yan kungiyar, reshen Jihar Zamfara da su rika zuwa ana zama da su, lokaci bayan lokaci.A nasa jawabin, shugaban kungiyar, Chif Chinedu Okoronko ya bayyana cewa nan ba da jimawa ba, za a kawo karshen wahalar karancin mai da ake fama da shi a kasan nan.
Shugaban ya kara da cewa, a halin da ake ciki yanzu kusan ko’ina an tura motoci wadanda suke daukar mai kuma ba tare da bata lokaci ba. Za a sami mai a fadin kasar nan.
Wannan ziyarar dai ta biyo bayan zaben da ’ya`yan kungiyar suka gabatar ne karkashin shugaban kungiyar ta kasa, duk da cewa zaben ya so ya gamu da tarnaki daga wasu bangare na mambobin kungiyar.
A halin da ake ciki yanzu dai, an zabi Alhaji Surajo Kamba a matsayin shugaban kungiyar. Zaben dai ya gudana ne a otel din Karama da ke Gusau, Babban Birnin Jihar Zamfara.