An yi kira ga sha’irai da su kyautata tarbiyyarsu
An yi kira ga mawakan yabon Manzon Allah (s.a.w) da su zamo masu neman ilimi kowanne, domin ba shi yiwuwa ka wake wani mutum daban ba tare da ka kusanci na jikinsa ko da fadawansa ba ne, domin samun wani abu nasa da za ka iya wakewa ba, ballantana Manzon Allah (s.a.w).Kamal Abdulkadir, khalifan Hussaini […]
An yi kira ga mawakan yabon Manzon Allah (s.a.w) da su zamo masu neman ilimi kowanne, domin ba shi yiwuwa ka wake wani mutum daban ba tare da ka kusanci na jikinsa ko da fadawansa ba ne, domin samun wani abu nasa da za ka iya wakewa ba, ballantana Manzon Allah (s.a.w).
Kamal Abdulkadir, khalifan Hussaini dannasarawa Jos, na kudancin Kaduna ne ya yi wannan kiran a lokacin da yake zantawa da Aminiya. Ya ci gaba da cewa kamar yadda ba za ka iya wake wanda ba ka san wani abu a kan shi ba, haka ba za ka iya isar da kowane irin sako na Musulunci ta hanyar wake ba, matukar ba ka da ilmin addinin da kake karewa.
Mawakin ya ci gaba da cewa: “Sannan wani abu muhimmi, shi ne tarbiyya. Ita kuma wannan ta shafi mai ilmi da marar ilmi, domin da zarar ka mayar da kanka mawakin yabon Manzon Allah (s.a.w), to ka zama abin koyi ne a wajen wasu. Don haka abin takaici ne a samu mawaki ba shi da tarbiyya ta gari, ko kuma ya zamo yana fadar abin da ba ya aikatawa,” Inji shi.
A karshe ya yi kira ga sha’irai da su zamo masu hadin kai da kaunar juna, sannan kuma ya yi kira ga shugabannin kungiyoyin mawakan Musulunci da su rika shirya musu gasa a tsakaninsu domin kara kwarin gwiwa da kusantar juna, musamman na reshen Jihar Kaduna.