An yi kutsen Naira biliyan 16 a kasafin ma’aikatar Fashola-Sanatoci
A jiya ne sanatoci suka gano kutsen kimanin Naira miliyan 16 da aka kasafta wajen yin wasu ayyuka marasa muhimmanci a kasafin kudin ma’aikatar Makamashi, Ayyuka da Gidaje, karkashin jagorancin Babatunde Raji Fashola. An bayyana hakan ne a lokacin da ministar a ma’aikatar, Mustapha Baba Shehuri ya bayyana a gaban kwamitin sanatocin a kan makamashi. […]

A jiya ne sanatoci suka gano kutsen kimanin Naira miliyan 16 da aka kasafta wajen yin wasu ayyuka marasa muhimmanci a kasafin kudin ma’aikatar Makamashi, Ayyuka da Gidaje, karkashin jagorancin Babatunde Raji Fashola.
An bayyana hakan ne a lokacin da ministar a ma’aikatar, Mustapha Baba Shehuri ya bayyana a gaban kwamitin sanatocin a kan makamashi.
Sanata Adamu Aliero, dan jam’iyyar APC mai wakiltar Kebbi, ne ya janyo hankalin sanatocin cewa akwai wasu ayyuka guda biyu da kudin da za su ci ya kai kimanin Naira biliyan 16 wadanda aka maimaita a kasafin kudin ma’aikatar ta Makamashi da kuma Kamfanin Rarraba Wuatar lantarki ta kasa (TCN).
“Biliyan 4 da biliyan 12 din nan ya fito a kasafin kudin TCN a lokacin da suka bayyana a gabanmu domin kare kasafin kudinsu. Me ya kawo kudin kuma nan? Akwai rudani gaskiya.”
Da yake mayar da jawabi, ministan sai ya ce kasafin kudin duk daya ne, amma sai sanata Abaribe ya ce, “A’a minsita, kasafin kudin ya bambanta, muna da kasafin kudin TCN.”
Shi ma mataimakin kwamitin, Sanata Bukar Mustapha daga Jihar Katsina sai ya ce “Abin da Aliero ya fada gaskiya abin damuwa ne. kasafin kudin aikin Kashimbilla baida alaka da ma’aikatan makamashi. Akwai wasu da yawa, wannan ne matsalar ma’aikatar makamashi…”
Hakanan kuma, sanatoci sun tabo bayanin kasafin kudin sayan motoci da ma’aikatar ta yi, wanda ya kai kimanin Naira miliyan 768.
Daga baya sai sanatocin suka dage zaman zuwa wani lokaci, bayan rashin gamsuwa da bayanan da minsitan ya musu.