An yi maraba da cire shingayen sojoji a kan hanyoyi
Mazauna Kaduna sun bayyana farin cikinsu da janye shingayen sojoji daga kan tituna da gwamnati ta yi, inda suka bayyana cewa hakan ya dace. Idan ba a manta ba shugaban kasa Muhammadu Buhari ne ya bada umurnin yin hakan jin kadan da komawarsa fadar shugaban kasa da ke Abuja a ranar litinin.Limamin Masallacin Titin Faki […]

Mazauna Kaduna sun bayyana farin cikinsu da janye shingayen sojoji daga kan tituna da gwamnati ta yi, inda suka bayyana cewa hakan ya dace.
Idan ba a manta ba shugaban kasa Muhammadu Buhari ne ya bada umurnin yin hakan jin kadan da komawarsa fadar shugaban kasa da ke Abuja a ranar litinin.
Limamin Masallacin Titin Faki da ke Tudun Wada, Kaduna Ustaz Aminu Abubakar, ya bayyana farin cikinsa game da wannan umurni da gwamnati ta bayar na janye shingayen sojoji daga kan tituna. A cewarsa, al’umma musamman masu ababen hawa na takuruwa da wannan shingaye. “ Kamar yadda ka sani ne, ni dai a ra’ayina ina ganin janye su daga kan tituna alheri ne ga jama’a, domin tun da aka saka su ba su taba kama kowa ba a Kaduna kuma ga shi sai takura jama’a da suke yi. Saboda haka muna murna da wannan mataki. Da fatan Allah Ya cigaba da kare mu,” inji shi.
A ganinsa ba za a samu matsala a kan haka ba, ‘’domin akwai ‘yan sanda da ke sintiri a kan tituna, saboda haka za su taimaka wajen samar da tsaro. In dai batun cire shingayen sojoji ne mutane na farin ciki da yin haka. Sai dai muna bukatar a kara jami’an tsaro a cikin al’umma,” inji shi.
Shi ma Barista Mohammad Bello Umar cewa ya yi, hakika dauke sojojin a kan titi ya dace, domin ba aikinsu suke yi ba. Ya ce aikin tsaron cikin gida na ‘yan sanda ne ba na soja ba, sojoji aikin tsaron kasa suke yi.
“Kuma sojoji a kwarewarsu ba su da fahimtar mu’amala da jama’a shi ya sa da mutum da ya dan yi masu kuskure daya sai su harbe shi. Sojoji yaki suka sani, amma yanzu ka ga sai su koma bariki a bar ‘yan sanda su cigaba da aikinsu,” inji shi.
Shi ma Bello Idris Dallaji a Kaduna cewa ya yi, janye shingen ya yi kyau, domin dama ba abin da suke yi illa takura wa masu ababen hawa a kan hanya. Mafi yawan lokuta idan ka samu kanka a a wannan shinge a cikin mota kukan dauki sa’o’i kuna bin layi ba tare da suna binciken komai ba. Saboda cunkoson ababen hawa sai ka ga har buga wa juna ake yi, kuma idan hakan ya faru su babu ruwansu. Sannan suna cutar da jama’a. A yanzu, musamman a jahar Kaduna mun fara samun walwala saboda babu sojoji a kan titi.
Abuja
Daga Abuja kuma wani mai suna Ibrahim Isma’il ya bayyana cewa, ‘’wannan abu ne da mu ka jima muna dako sai yanzu Allah Ya kawo lokaci. A baya a kullum sai na kashe sama da sa’a biyu daga garin Nyanya inda nake da zama zuwa wajen aikina da ke cikin birnin Abuja, amma abin mamaki sai ga shi ina isowa ofis cikin minti talatin a yanzu. Dama Shingayen nan ba abin da suka haifar in banda cunkoso. Na tabbata shugaban kasa bai bada umarnin ba sai bayan da ya yi zama da shugabannin tsaro, kuma a matsayinsa na masani a harkan tsaro ba ni da fargaba a kan matakin da ya dauka a kan wannan al’amari.’’
Shi ma Usman Kamba a Abuja cewa ya yi, na yi farin ciki da daukar wannan mataki,domin baya ga cunkoso da yake haddasawa, jami’an tsaro da ke sa ido a wuraren shingayen na kuntata wa mutane. Bai wuce kamar mako biyu ba aka harbe wani direba a ire-iren wadannan wurare da ke wajen garin Kaduna a kan Naira dari biyu, sannan ga shi ana wucewa da marasa lafiya ta wurareren nan da ke bukatar kaiwa ga asibiti a cikin hanzari, ga kayan abinci masu saurin lalacewa da ake asararsu, ga dabbobi. Daga nan Abuja zuwa Kano, wanda hanya ce da na ke bi akai-akai, ba karamar wahala mu ke sha ba a lokacin da shingayen su ke, amma sai ga shi a yanzu cikin awa hudu mutum ya isa Kano daga Abuja.
Haka shi ma Malam Gambo Hassan ya ce, ‘na goyi bayan cire wadannan shingayen, mu ’yan kasuwa da ke yawan yin tafiye- tafiye mun fuskanci kunci matuka a lokacin da shingayen su ke, motocinmu kan lalace a saboda daukar zafi, mai da za ka ririta na kwana uku misali, sai ya kare a yini guda a sakamakon cunkoso. Cire su zai bunkasa tattalin arziki a yankunanmu, harkokinmu su dawo. Kuma ba mu da wata fargaba na cire shingayen, kariya ta Ubangiji mu ke fata, zamansu a wuraren bai hana masu kai hare-hare yin ta’addacinsu ba, kuma muna fata Allah Ya taimaki wannan gwamnatin tamu ta samu nasarar kawo karshen wannan matsala gaba daya.
Shi ma Sirajo Musa Bakoji ya ce cire shingayen ya yi daidai, saboda da shinge da rashinsa kusan abu guda ne, a game da matsalar tsaro da muka yi fama da ita kuwa, dama ba wani bincike da su ke yi sai dai kawai jawo tsaikon tafiya da kuma takura wa jama’a wadanda ba su ji ba ba su gani ba, su ko wadanda aka ce ana tsare hanyar saboda su ban jin za su bi wadannan hanyoyin kasancewar sun san matsayinsu idan suka shiga hannu.
Maiduguri
Malam Abba Aji, wani direba ne a garin Maiduguri, ya bayyana cewa,’’Ai mu mun fi son a cire wannan shingayen domin suna damunmu da karbar kudi, kuma ga shi ba sa magance matsalar tsaron da yake addabarmu. Saboda hakane muke rokon Shugaba Buhari da ya soke mana wannan shingaye a wannan yanki, domin mu a gare mu ba shi da wani amfani, kuma wani lokacima suna bata mana lokaci, domin tafiyar da za ka yi cikin mintoci 30 a da, amma a yanzu sai ka yi sama da sa’o’i biyu, saboda haka muna goyon baya tare da rokon a cire mana wadannan shingaye.’’
Hajiya Falmata, wata ‘yar kasuwace a garin Maiduguri, ta ce, ‘’Don Allah Shugaba Buhari ka yi mana rangwame ka sa a cire mana wadannan shingayen, domin mu a wajenmu ba su da wani amfani, don suna kawo mana tsaiko a harkokin kasuwancinmu. A da mun ji an ce a cire a duk kasa, amma sai muka ji kuma ban da nan bagarenmu na Arewa Maso Gabas. Duk da cewa matsalar tsaro ya addabe mu, amma muna rokon gwamnati da ta yi wa Allah a cire mana wannan shinge don samun bunkasuwar kasuwancinmu.’’
Shi ma Alhaji Sani Ibrahim, cewa ya yi, ‘’Barin wadannan shingaye ba alheri ne ga al’ummar yankin Arewa Maso Gabashin kasar nan ba, domin kuwa ta wannan wurin ne ake yawan kai hare-hare, kuma bai yiwuwa a ce a cire na wani bangare kuma a ce ba a cire na wani bangare ba. Amma muna roko ga shugaban kasa Buhari da ya yi wa Allah ya cire mana wannan shingayen, don cirewar shi ne ya fi mana, an kirkiro su ne don a takura mana.’’
Shi kuwa Malam Musa, wani mazaunin garin Maiduguri cewa ya yi, ‘’Cire wadannan shingaye babu amfani gara a barsu, domin ta haka ne jami’an tsaro ke gudanar da ayyukansu na tsaro, ai in ba don akwai su ba to da yanzu garin Maiduguri ya cika da ‘Yan ta’adda, za su samu damar shigowa su yi mana barnar rayuka da dukiyoyinmu, to amma ka ga da ba su samu sakewaba ai ba su iya sun shigo ba. Saboda haka wannan wani kariya ne na daban.
Maganar karbar kudi kuwa, wannan wani abu ne daban, kuma ai ba sa matsawa su karbi kudi a wajen kowa, sai wanda ya ga dama sannan zai ba su. Amma indai maganar gaskiya ake ,so suna taimaka wa kasa. Ko nawa ne mutum ya ba su ai ba wani abu ba ne, tunda yake dai suna aikin tsaron rayukanmu ne, ni dai ban ga wani abu ba.’’