An yi masa wanka da guba a kan Naira dubu

Kimanin kwana 40 da suka gabata ne aka yi wa wani dan acaba mai suna Isah Abdullahi wanka da ruwan batir a lokacin da yake gudanar da sana’arsa a Abuja.Miyagun fasinjojin sun yi masa wanka da ruwan batir ne a kan Naira dubu daya wanda hakan ya jawo rabin kansa da fuskarsa da idanuwansa suka […]

An yi masa wanka da guba a kan Naira dubu
An yi masa wanka da guba a kan Naira dubu

Kimanin kwana 40 da suka gabata ne aka yi wa wani dan acaba mai suna Isah Abdullahi wanka da ruwan batir a lokacin da yake gudanar da sana’arsa a Abuja.
Miyagun fasinjojin sun yi masa wanka da ruwan batir ne a kan Naira dubu daya wanda hakan ya jawo rabin kansa da fuskarsa da idanuwansa suka samu tawaya.
Lamarin ya faru ne a Unguwar Lugbe cikin Abuja inda Isah ya dauki wasu matasa biyu zuwa wani wuri a cikin unguwar a kan Naira 100. Bayan sun isa ne suka nemi ya ba su Naira 900 bisa cewa Naira dubu daya ce a hannunsu.
Sai dai ya ce bayan sun karbi kudin sai suka yi kokarin tafiya ba su ba shi Naira dubun ba, don haka ya matsa su ba shi, inda daya daga cikinsu ya bude wata karamar jarka ya kwara amsa abin da ke ciki ya fadi kasa yana ihu.
Matashin mai kimanin shekara 20 ya ce, “Yana watsa min abin sai na ji kamar kwakwalwata tana tafasa nan da nan na fadi a kasa ina ihu. Har sun yi niyyar daukar babur dina sai suka ji motsin mutane suna zuwa don haka suka gudu. Daga nan aka kira ’yan uwana suka dauke ni zuwa asibiti.”
dan acabar wanda ke kwance a Asibitin Malam Aminu Kano ya ce ya shafe awa 12 kafin likita ya taba shi, saboda an kai shi asibitoci hudu a Abuja, amma ba su karbe ni ba. “Da karfe 11 na dare da ‘yan uwana suka ga wahalar da nake sha ne suka dauko shatar mota suka taho da ni Kano suka kai ni Asibitin Murtala na zauna mako uku daga bisani a dawo da ni nan,” inji shi.  
dan acabar wanda dan asalin karamar Hukumar Rimin Gado ne ya ce bai taba yin acaba sai da ’yan uwansa suka ja shi zuwa Abuja.
Ya yi kira ga gwamnati da masu hannu da shuni su taimaka wajen daukar nauyin jinyarsa saboda iyayensa ba su da  karfi, kuma ana bukatar kusan Naira miliyan uku don yi masa a iki a gida da kasar waje. “Tunda na zo asibitin jama’ar Annabi ke daukar nauyin jinyata, iyayena ba su da karfi,” inji shi.
Dokta Bashir Mohammed Ibrahim na Asibitin Malam Aminu Kano ya ce za su gudanar da aiki kashi hudu ga Isah kafin a yi masa wani aikin a kasar waje.