An yi nasarar raba tagwayen da aka haifa a manne da juna a Adamawa
Shugaban Cibiya Lafiya ta Gwamnatin Tarayya da ke Yola Jihar Adamawa, Farfesa Awwal Muhammad ya ce da shi da tawagarsa sun samu nasarar raba wasu tagwaye da aka haifa a manne da juna. Farfesan wanda ya bayyana haka a Yola yayin bikin murnar raba sun ya ce wannan shi ne karo na uku da suke […]
Shugaban Cibiya Lafiya ta Gwamnatin Tarayya da ke Yola Jihar Adamawa, Farfesa Awwal Muhammad ya ce da shi da tawagarsa sun samu nasarar raba wasu tagwaye da aka haifa a manne da juna.
Farfesan wanda ya bayyana haka a Yola yayin bikin murnar raba sun ya ce wannan shi ne karo na uku da suke samun nasarar yin aikin.
Ya ce sun samun yin aikin ne sakamakon tallafin da suka samu daga Sakataren Gwamnatin Tarayya Boss Mustapha da Gidauniyar Emeka da kuma Hukumar Dake Kula da Bututan Iskar Gas ta Kasa (NLNG) wadanda suka bayar da tallafin kayan tiyatar.
Ya ce Cibiyar Kula da Lafiya ta Gwamnatin Tarayya da ke Yenagoa a Jihar Bayelsa ce ta bukaci a raba ‘yan biyun amma kalubalen sufuri ya nemi zama musu kalubale saboda za su iya fuskantar matsala in aka tafi da su a mota.
A kan haka ne shugaban asibitin ya tuntubi Babban Hafsan Sojin Sama na Kasa Sadique Abubakar ya tallafa aka yi jigilar jariran lokacin suna kwana 23 da haihuwa.
Farfesa Awwal wanda ya ce an yi wa jariran tiyatar ne a hantarsu ya kuma yaba wa wani asibitin kasar Jamus bisa ba su damar yin amfani da injinansu wajen tiyatar a kyauta.
Ya kara da cewa an yi aikin ne a ranar 20 ga watan Agusta inda jariran suke samun sauki cikin gaggawa, yana mai cewa an sallame su ne kwana biyar da kammala aikin.
A nasa tsokacin, Gwamnan Jihar Adamawa, Ahmad Umar Fintiri ya yaba wa tawagar kwararrun da ta gudanar da aikin karkashin jagorancin shugaban asibitin wanda ya kai ga ceto rayuwar jariran.