An yi rashin Sarkin Karshi

A ranar Talatar da ta gabata ne Allah Ya yi wa Sarkin Karshi Dokta Muhammadu Bako II rasuwa bayan doguwar jinya. Sarkin Mai daraja ta daya ya rasu ne a fadarsa a garin Karshi da ke karamar Hukumar Karu a Jihar Nasarawa da misalin karfe 7:00 na safe, kuma an yi jana’izarsa kamar yadda addinin […]

An yi rashin Sarkin Karshi
An yi rashin Sarkin Karshi

A ranar Talatar da ta gabata ne Allah Ya yi wa Sarkin Karshi Dokta Muhammadu Bako II rasuwa bayan doguwar jinya. Sarkin Mai daraja ta daya ya rasu ne a fadarsa a garin Karshi da ke karamar Hukumar Karu a Jihar Nasarawa da misalin karfe 7:00 na safe, kuma an yi jana’izarsa kamar yadda addinin Musulunci ya tanada a ranar.
Jana’izar marigayin ta samu halartar manyan mutane daga sassan kasar nan, cikinsu har da Gwamnan Jihar Nasarawa Alhaji Umaru Tako Al-Makura, wanda ya kwatanta marigayi da mutumin kirki mai son zaman lafiya da son al’ummarsa. Gwamnan ya ce “Ina yi wa marigayi fatar dacewa da makoma mai kyau kuma ina yi wa magadan sarautar wannan fada fatan alheri.”
Shugaban kungiyar Fulani Makiyaya ta Miyatti Allah Kautal Hore ta kasa kuma shugaban Kamfanin Ruwa na Maliya, Alhaji Abdullahi Bello bodejo ya jajanta wa iyalan marigayin, inda ya ce “ina yi wa marigayi Sarkin Karshi Dokta Muhammadu Bako II, babanmu mai daraja da adalci fatar Allah Ya jikansa ya sa ya dace da makoma mai kyau.”
Shugaban karamar Hukumar Karu, Alhaji Yahaya Iya Mu’azu, ya ce “Zai yi wuya a samu Sarki irin Muhammadu Bako, babu abin da zan iya cewa sai dai in yi masa fatar Allah Ya jikansa da rahama, Ya sa ya dace da Aljannatul Firdausi, magada kuma Allah Ya ba su hakurin rashin kuma ya ba su Sarki nagari kamar marigayin.”