An yi rikici tsakanin ’yan Izala da Shi’a a Ringim
Mutane biyar ne suka jikkata, yayin da kuma aka kama wasu mutanen biyar, a sakamakon wani rikici mai nasaba da addini da ya barka a Kwalejin Nazarin Addini da Shari’a da ke Ringim, Jihar Jigawa, a ranar Talata da ta gabata. Rikicin ya faru ne tsakanin dalibai ’yan kungiyar Izalatul Bid’a Wa’ikamatus Sunna da kuma […]
Mutane biyar ne suka jikkata, yayin da kuma aka kama wasu mutanen biyar, a sakamakon wani rikici mai nasaba da addini da ya barka a Kwalejin Nazarin Addini da Shari’a da ke Ringim, Jihar Jigawa, a ranar Talata da ta gabata.
Rikicin ya faru ne tsakanin dalibai ’yan kungiyar Izalatul Bid’a Wa’ikamatus Sunna da kuma takwarorinsu mabiya Shi’a, dukkansu da ke karatu a makarantar.
Jami’in hulda da jama’a na rundunar ’yan sanda na Jihar Jigawa, DSP Audu Jinjiri ya tabbatar da faruwar lamarin. Ya ce lamarin ya faru ne a daidai lokacin da ’yan kungiyar Izala suke gabatar da wa’azi a makarantar, a cikin masallaci, abin day a sanya suka tare hanyoyin da ke harabar masallacin. Su kuma ’yan kungiyar Shi’a suka je wucewa, inda suka ce ala tilas sai sun wuce ta harabar wurin, alhalin an hana bi ta cikin harabar da ake gudanar da wa’azin.
Ya kara da cewa rundunar ’yan sanda ta kira duk bangarorin biyu, ta zauna da su; ta kuma zauna da shugabannin makarantar da sauran duk masu ruwa da tsaki a makarantar da jama’ar gari domin ganin kawo karshen matsalar.
Jinjiri ya ce yanzu haka sun baza jami’an tsaro ciki da wajen makarantar, domin kare rayuka da dukiyar jama’a daga fuskantar shiga mawuyacin halin rayuwa. Suna ta kokarin murkushe wutar rikicin da take neman ruruwa a makarantar.