An yi rub-da-ciki wajen rabon abincin azumi a yankin kaura – Sahabi Liman

An bayyana cewa duk da kokarin da gwamnatin Jihar Zamfara ta yi na samar da tallafi ga marasa karfi a watan azumin da ya gabata, masu rabon kayan sun yi rub-da-ciki kan kayan tare da kara wa masu karfi karfi a karamar Hukumar kauran Namoda.Wannan koke ya fito ne daga daya daga cikin shugabannin Jam’iyyar […]

An yi rub-da-ciki wajen rabon abincin azumi a yankin kaura – Sahabi Liman
An yi rub-da-ciki wajen rabon abincin azumi a yankin kaura – Sahabi Liman

An bayyana cewa duk da kokarin da gwamnatin Jihar Zamfara ta yi na samar da tallafi ga marasa karfi a watan azumin da ya gabata, masu rabon kayan sun yi rub-da-ciki kan kayan tare da kara wa masu karfi karfi a karamar Hukumar kauran Namoda.
Wannan koke ya fito ne daga daya daga cikin shugabannin Jam’iyyar ANPP mai mulkin jihar, Alhaji Bashir Sahabi kaura yayin da yake zantawa da wakilinmu a Gusau, bayan ya raba wata takardar koke ga manema labarai dauke da sa hannunsa.
Ya ce su jama’ar kauran Namoda ba su gamsu da yadda kwamitin rabon hatsin ya raba kayan ba, domin a cewarsa wasu manya a ckaramar hukumar sun karbi kayan tallafin daga jiha kuma sun karba daga karamar hukuma.
Ya ce ana zargin ’yan kwamitin da raba wa kawunansu wani kaso daga cikin kayan abincin da ya dace su raba wa mabukat kamar yadda gwamnati ta ba da umarni, amma sai ga shi wasu masu rabon su ne suka samu kaso mafi tsoka, musamman kwamishinoni da masu ba da shawara da kuma shugabannin jam’iyya a jiha da wasu masu fada-a-ji a garin na kaura.
Sahabi ya ce kimanin buhu 55,875 ne tsakanin shinkafa da sukari da gero da dawa da masara ake zargin sun yi batan dabo tsakanin ’yan kwamitin da masu fada-a-ji da ke kauran Namoda, sai kuma atamfofi da yadin shadda 25,375 suka yi batan dabo, sabanin yadda gwamnati ta ce a ba da su.
Alhaji Bashir ya nemi Gwamna Abdul’aziz Yari ya dubi wannan koke da idon basira, ya nada kwamiti don binciken yadda aka yi rabon. Kuma ya nemi idan gwamnati za ta bada bubura da kudin tallafi ga mata, ta sake wasu mutane wadanda ake ganin za su yi adalci.
Lokacin da wakilinmu ya nemi jin ta bakin shugaban kwamitin rabon hatsin Alhaji Abubakar idris kan badakalar da ake zarginsu da ita, ya ce gwamnati ta ba su ka’idojin rabon wannan kaya, kuma shi suka bi, kuma sun raba yadda ya dace su raba.