An yi ruwan kankara zalla a Taraba
Kankarar ce zalla ta rika sauka, babu ruwa
An yi ruwan kankara zalla a garin Nguroje da ke karamar hukumar Sardauna a tsaunin Mambilla na Jihar Taraba.
An yi ruwan ne a ranar Talata kuma an kwashe kimanin awa daya ana yin shi ba tare da saukan ruwa irin wanda aka saba gani ba.
- Kotu ta sa a daure matashi a Kano kan zargin damfarar miliyan 30
- Boko Haram ta yi wa masunta 7 yankan rago a Tafkin Chadi
Wani mazaunin garin na Nguroje mai suna Abdulrashid Jobbdi ya shaida wa Aminiya cewa wannan lamari ya bai wa mazauna garin mamaki.
A cewarsa, ba su taba samun ruwan na kankara zalla ba, sai dai akan sami saukar kankara a lokacin ruwan sama.
“Amma yau a maimakon ruwan sama, sai kankara zalla ta sauka,” a cewar Abdulrashid.