An yi sabuwar masarauta a garin Iwaya, Legas

Garin Iwaya ya samu sabuwar masarauta yayin da a ƙarshen makon jiya Sarkin Hausawan Legas, Alhaji Sani Kabiru ya naɗa Sarkin Hausawan garin na Iwaya, Alhaji Muhammadu Bashiru da jakadiyarsa, Hajiya Maryam Sallau da hakimansa guda 15.A cewar magatakardar sabuwar masarauta, wanda kuma shi ne Maji Daɗin garin Iwaya, Sulaiman Ahmad, dalilansu na neman a […]

An yi sabuwar masarauta a garin Iwaya, Legas
An yi sabuwar masarauta a garin Iwaya, Legas

Garin Iwaya ya samu sabuwar masarauta yayin da a ƙarshen makon jiya Sarkin Hausawan Legas, Alhaji Sani Kabiru ya naɗa Sarkin Hausawan garin na Iwaya, Alhaji Muhammadu Bashiru da jakadiyarsa, Hajiya Maryam Sallau da hakimansa guda 15.
A cewar magatakardar sabuwar masarauta, wanda kuma shi ne Maji Daɗin garin Iwaya, Sulaiman Ahmad, dalilansu na neman a kafa sabuwar masarauta a garin shi ne, domin a ƙara samun haɗin kai a tsakanin ’yan Arewa mazauna yankin. “A wani lokaci da ya gabata ne Allah Ya yiwa wani dan Arewa rasuwa, a wannan lokacin sai ya zamana Yarabawa ne suka ba shi duk wani taimakon da mamaci yake buƙata. Ganin hakan ne ya sanya mu muka ga ya kamata mu kafa kungiyar taimakon kai da kai sai muka kai wa Sarkin Legas maganar. Ya ba mu shawarar cewa mu nemi masarauta domin sau da yawa ana kafa ƙungiya tana watsewa. Haka kuma aka yi, muka bi duk ƙa’idojin da ake bi a sami sarauta a wannan yankin. Sai ga shi Allah Ya ba mu. Fatanmu a nan shi ne, mu sami hadin kan duk jama’armu, domin ci gaban wannan gari namu.” Inji Maji Daɗi.
A cewar sabon sarkin Iwaya, Alhaji Muhammadu Bashiru, su ’yan Arewan yankin zaune suke lafiya da abokan zamansu Yarabawa, ba tare da wata matsala ta ɓangaranci ko wariya ba. Don haka ya gode wa Allah da Ya yi musu baiwa da sabuwar masarautar. Haka kuma ya yi kira ga daukacin hakimansa da su yi aiki tuƙuru bisa gaskiya da amana, kana ya ba al’ummar garin tabbacin cewa zai ci gaba da hidimta masu kamar yadda ya saba tun kafin a ba shi wannan sarautar. Don haka ya nemi haɗin kansu baki daya domin ci gaba da samun zaman lafiya a yankin.