An yi shagulgulan farin ciki a Kudancin Najeriya
An gudanar da shagulgulan murna da canjin mulki da aka samu daga jamiyar PDP zuwa APC, a jihohin Kudu maso gabashin kasar nan cikin kwanciyar hankali da lumana sai dai abin ya dauki sabon salon a yi wa juna fatar alheri da kuma barka da arziki da wannan sauyi da Allah Ya kawo. Binciken da […]
An gudanar da shagulgulan murna da canjin mulki da aka samu daga jamiyar PDP zuwa APC, a jihohin Kudu maso gabashin kasar nan cikin kwanciyar hankali da lumana sai dai abin ya dauki sabon salon a yi wa juna fatar alheri da kuma barka da arziki da wannan sauyi da Allah Ya kawo.
Binciken da Aminiya ta gudanar a jahohin Akwa Ibom da Ribas da kuma Enugu, ta gano cewa duk ilahirin inda ’yan asalin Arewa ke gudanar da huldodin kasuwanci, ba su yi wani bidiri ba da suka hada da kide-kide da bushe- bushe ba.
Tun farko, shugabannin al’umma da na addini suka gargadi ’yan Arewa mazauna wadannan jihohi da kada su fito su yi wani shagali ko nuna farin cikinsu karara a fili, domin gudun kada dacin faduwar zabe da dan yankinsu ya yi abun ya rikide ya koma fada.
A Jihar Akwa Ibom, Malam Ababa Abba Ladan ya tabbatar wa wakilinmu cewa: “Ai mu a nan Akwa Ibom, mun bi wuraren ibada da kasuwanni da ’yan Arewa suke mun ja kunnensu cewa kada su kuskura su yi wani shagali bare hakan ya jawo wata fitina. Don haka mu mun rika yi wa juna murnar ce da kuma fatan alheri tare da yi wa shugaban addu’ar Allah Ya yi masa jagora.”
A Jihar Ribas kuwa, Alhajin Garba dangetso ya shaida wa Aminiya cewa: “Mu dai a nan unguwar masana’antu ta babbar mayankar Fatakwal, mun rika yi wa juna barka da kuma fatar alheri amma mu ba mu yi bidiri da kide-kide ba, kamar yadda aka rika yi a wasu jihohi na Arewa. Fatarmu a nan, Allah Ya taya shi sabon shugaban mai jiran gado riko.”
Haka kuma akasarin ’yan asalin Kudu maso kudu, kamar yadda bayanai suka riske mu, sun yi nuni da cewa tun daga lokacin da aka rika bayar da sakamakon zaben jikinsu ya rika yin sanyi har zuwa lokacin da suka samu labarin Shugaban kasa mai barin gado, Goodluck Jonathan ya kirawo Janar Muhammadu Buhari ya taya shi murna, shi kuma ya rungumi kaddara kamar an zare masu laka a jiki.
A Kalaba kuma sai a ranar Laraba ce jamiyyar APC ta jihar ta fita zagayen murnar nasara zaben da ta samu karkashin jagorancin shugaban jam’iyyar, Usani Usani da kuma Odey Ochicha da Effiong Ekarika, wanda aka fi sani da suna Obama, dan takarar mukamin Gwamna da na majalisar jiha da sauran manyan jam’iyyar a jihar ne suka fita cikin lumana suna zagaya wasu sassan gari.
A sakonsa ga magoya bayan jam’iyya da kuma Shugaban kasa mai jiran gado, Alhaji Babangida Umar Shugaban Jamiyyar APC, mazaba ta daya, ya gode wa ilahirin magoya bayansu da suka zage damtse suka ga an kai ga cin ma nasara. Da ya juya kan Shugaban kasa mai jiran gado, wato Janar Muhammmadu Buhari, ya shawarce shi ya rungumi duk wadanda ba su zabe shi ba, a tafi a tare domin a yi wa kasa aiki. Sannan kuma ya mayar da hanakali wajen shawo kan matsalar tsaro kuma ya yafe wa duk wani wanda ya yi masa batanci ko yarfen siyasa domin a bambance tsakanin dan duma da na kabewa.
Abun farin ciki ga wadanda suka tofa albarkacin bakinsu, sun gode wa Allah da aka yi zaben da bayar da sakamakon lafiya ba tare da an kashe ko da dan kaza ba.