An yi son-rai a daukar daliban Kwalejin Hafsoshin Najeriya
Jerin sunayen wadanda suka samu nasara da masu zaman jiran tsammani na daliban da aka dauka a kwas na 65 na Kwalejin Horar da kananan Hafsoshin Soja (NDA) da ke Kaduna da za su samu horon karamin zango da masu karatun digiri yana jawo cece-ku-ce.Aminiya ta gano cewa ana buga jerin sunayen a kafafen watsa […]

Jerin sunayen wadanda suka samu nasara da masu zaman jiran tsammani na daliban da aka dauka a kwas na 65 na Kwalejin Horar da kananan Hafsoshin Soja (NDA) da ke Kaduna da za su samu horon karamin zango da masu karatun digiri yana jawo cece-ku-ce.
Aminiya ta gano cewa ana buga jerin sunayen a kafafen watsa labari sai aka fara samun korafe-korafe, sakamakon zargin cewa an keta ka’idar raba-daidai ta Tarayya, zargin da mahukuntan soja suka musanta.
Tsarin raba daidai kamar yadda yake kunshe a cikin tsarin mulkin kasar nan, ya bukaci a tabbatar da cewa nada mukamai da daukar aiki a hukumomi da cibiyoyin gwamnati ya samar da wakilci ga bangarori mabambanta na kasar nan.
Sai dai bayan buga jerin sunayen wadanda aka dauka a cibiyar horar da sojojin ke da wuya, sai Majalisar Limamai da Malaman Musulunci ta Jihar Kaduna ta gudanar da wani taro, inda ta tattauna batutuwa da dama ciki har da daukar sojojin da sauran ma’aikatan gwamnati.
Taron ya nazarci yadda aka dauki sojoji musamman a Kwalejin NDA, inda ya nuna damuwa kan yadda aka nuna karkata ga wani bangare a yayin daukar.
Mahalarta taron sun yi ittifakin fitowa fili su bayyana rashin amincewarsu kan rashin adalcin da aka nuna wajen daukar sojoji a Kwalejin NDA, inda suka kafa hujja da daliban kwas na 65. Sun ce akwai wani shiri da gangan na a tauye matasa Musulmi a wannan bangare.
Shugaban Majalisar koli kan Harkokin Shari’a a Najeriya reshen Jihar Kaduna, Sheikh Zubairu Sirajo da Shugaban Majalisar Limamai da Malamai ta Jihar, Sheikh Abubakar Babantine ne suka yi jawabi ga manema labarai bayan kammala taron inda kuma suka fitar da jawabin hadin gwiwa.
Jawabin hadin gwiwar ya bayyana cewa: “daukar daliban kananan hafsoshi a Kwalejin NDA na baya-bayan nan da aka buga a jaridar Daily Trust ta ranar 23 ga Agusta, 2013 yana da girgizarwa kuma abu ne da ba wata al’ummar da ta san abin da take yi da za ta lamunci haka. Sakamakon ya nuna an yi muguwar tauye al’ummar Musulmin Najeriya, kuma muna ganin wani shiri ne da ake yi a hankali domin a dakile matasanmu Musulmi daga shiga aikin soja da sauran hukumomin tsaro a Najeriya.
“Musulmin Kaduna musamman sun cancanci a yi musu bayani kan dalilin da ya sa cikin mutum 11 da aka dauka a Kwalejin NDA a bana, Musulmi biyu ne kacal aka dauka,” inji takardar.
Sheikh Babantine ya yi kira ga mahukunta a fannin tsaro da sauran hukumomin da alhakin daukar sojoji da sauran jami’an tsaro ke wuyansu, kan su rika yin adalci ga kowa kuma su hanzarta gyara lamarin. Ya kara da cewa: “Kuma muna kira ga Majalisar Dokoki ta kasa ta hanzarta duba daukar daliban Kwalejin NDA da sauran cibiyoyi irinta da niyyar tabbatar da adalci a tsakanin jama’ar kasa.”
Jerin sunayen daliban da suka samu nasarar shiga Kwalejin NDA kwas na 65 an sake shi ne a cikin watan Agusta, yayin da aka saki jerin sunayen wadanda za su samu horo na gajeren zango ya fito a wannan wata.
Aminiya ta gano cewa an zabi masu neman shiga kwalejin 13 zuwa 14 daga kowace jiha ciki har da masu jiran tsammani uku domin yin kwas na 65, yayin da aka ba Birnin Tarayya gurbin mutum 10.
Masu korafin sun kawo misali da jihohin Kaduna da Taraba da Bauchi da Borno da Gombe da Kebbi da kuma Adamawa wuraren da ake raba mukaman ma’aikatan da ake dauka a tsakanin Musulmi da Kirista, inda kuma aka danne Musulmin. Malam Murtada Mohammed ya soki jerin sunayen da ya bayyana marar adalci kuma marar daidaito, inda ya nuna mamaki kan yadda babu koda Musulmi daya da aka dauka daga Jihar Filato, alhali hatta Jihar Benuwai ta ba Musulmi daya dama.
Kwamandan Kwalejin NDA, Manjo Janar Chukwuemeka Onwameagbu ya shaida wa wakilinmu cewa aikin kwalejin shi ne bayar da horo ga daliban da suka samu nasara, amma ba a tsoma su a harkar daukar daliban.
“Ba a tsoma kwalejin a harkar zaben dalibai, aikin kwalejin ya takaita ne ga bayar da horo ga wadanda Hukumar Tantancewa ta Soja da Hedkwatar Soja ta kasa ta kafa ke zaba, kuma hukumar ta kunshi wakilai daga bangarorin soja uku da Ma’aikatar Tsaro,” inji shi.
Da aka tambaye shi kan ka’idojin da ake bi kafin a samu shiga kwalejin, Kwamandan ya nemi wakilinmu ya duba kafar sadarwar intanet ta NDA wato (nda.edu.ng) inda ya ce an bayyana dalla-dallar ka’idojin a ciki.
Aminiya ta kuma tuntubi Daraktan Labarai na Hedkwatar Sojan Najeriya Birgediya Janar Chris Olukolade. A sakon tes da ya aiko wa Aminiya ya ce, “Dukkan bangarorin da suke da muhimmanci ga raba daidai a kasa an bi su, kamar yadda tsarin mulki ya nuna a yayin wannan aiki. Duk wanda yake kokarin kawo bayanai na bangaranci marasa tushe ya nemi hakan ta wata hanyar.”
Ya ce, “Rundunar Sojan tana sane da muhimmancin kiyaye ka’idojin raba daidai kuma za ta ci gaba da yin aiki da su yadda ya kamata a kowane lokacin daukar aiki. Muna kira ga mutanen da suke da wasu bukatu na daban kada su shigo da batutuwan da za su kawo rarrabuwa a harkar soja.”
Wata majiya ta soja ta ce aikin Hukumar Tantancewar ce ta tabbatar da daidaita al’amura yayin daukar sojojin, inda ta kara da cewa, a yayin daukar aikin soja ana fifita cancanta a kan dukkan sauran ka’idojin. Kuma aikin Hukumar Tabbatar da Daidaito ta Tarayya ce ta daddale duk wani daukar aiki tare da bayar da shawarwari.
Jerin sunayen wadanda suka samu nasara da masu jiran tsammani don shiga Kwalejin NDA kwas na 65 na jihohin Kaduna da Adamawa da Borno da Taraba:
Kaduna
1. Yakubu Samuel
2. Anthony Bernard Kazah
3. Dabo Jesse Miracle Kazachat
4. Bako Ghabnom Stephen
5. Maigamu Martins Andrew
6. Laah Nicholas Bayo
7. Abdullahi Muhammad Bada
8. Abong Charles Tabat
9. Chinylo Shionwap Darius
10. Bello Fahd Tukur
11. Aliyu Jennifer
Masu jiran tsammani:
12. Dunia Elnathan Joshua
13. Parisa Elijah Kunsinmi
14. Abdul Abdullahi
Adamawa
1. Jeremiah Ayuba Medugu
2. Wesley Ishaku
3. Fidelis Emmanuel
4. Fadazyi Joseph
5. Charles Edward Ndappi
6. Bazza Murtala Yerima
7. Adams Chimda Abdullahi
8. Mustafa Bashiru Lawan
9. Jimpilda Peter Ijabula
10. Tumba Mercy Esther
Masu jira tsammani:
11. Mosu Rapha Phanuel
12. Nedison Sohanungti
13. Abubakar Muhammad Baba
Taraba
1. Suleman Amos Tayeri
2. Ahmed bictor Loh
3. Abba Asaph
4. Tsokwa Martins Tsokwa
5. Anthony Tswenbuma
6. Paul Atijwamrinam
7. Sani Hamdy Adamu
8. Bala Mona Noah
9. Ahmad Umar Abubakar
10. Aondoakaa Benjamin Terungwa
Masu jiran tsammani:
11. Iliya Headman Miji
12. Anthony John Ante
13. Yakubu Ismail
Borno
1. Ali Usman Kolo
2. Adamu Saidu Ibrahim
3. Wabekwa Joseph Sani
4. Ibrahim Umaru Hassan
5. Mshelia Mustapha Abdullahi
6. Ibrahim Aliyu
7. Daniel Dabid Dawa
8. Yakubu Timothy Tahir
9. Gadzama Yusuf Salihu
10. Adams Hanna Halima
Masu jiran tsammani:
11. Mamza Stephen Patrick
12. Isa Muhammed Awwal
13. Sarki Mustapha Bitrus