An yi taro kan cutar kansa a Kano
A kwanakin baya ne kungiyar Yaki da Ciwon Kansa (Daji) ta Cibil Society for Cancer Eradication (CiSCANEN) ta bi sahun sauran kungiyoyin duniya inda ta gudanar da bikin ranar yaki da ciwon wanda ya gudana a dakin taro na cibiyar kasar Amurka da ke dakin karatu na Murtala Mohammed da ke Kano.A lokacin taron, masana […]
A kwanakin baya ne kungiyar Yaki da Ciwon Kansa (Daji) ta Cibil Society for Cancer Eradication (CiSCANEN) ta bi sahun sauran kungiyoyin duniya inda ta gudanar da bikin ranar yaki da ciwon wanda ya gudana a dakin taro na cibiyar kasar Amurka da ke dakin karatu na Murtala Mohammed da ke Kano.
A lokacin taron, masana kan fannin kiwon lafiya sun gabatar da jawabai da kuma amsa tambayoyin al’umma da suka halarci taron.
Dokta Usman Bello na sashen kula da ciwon daji na asibitin koyarwa na Malam Aminu Kano shi ne ya gabatar da lacca kan yanayin kamuwa da ciwon da kuma laccar kan hanyoyin magance cutar da kuma hanyoyin kaucewa kamuwa da ita.
Har ila yau, an yi kira ga al’umma da su rika kokarin tuntubar masana dangane da duk wani abu da ya shige masu duhu kan ciwon na daji.
Jagorar kungiyar reshen Jihar Kano kuma Mataimakiyar Shugaba ta kasa Hajiya A’ishatu Halliru, wadda ta ce ciwon daji yana bukatar kulawa ta musamman, don haka nema suka kafa wannan kungiya ta CiSCANEN domin taimakawa kokarin gwamnati na “kakkabe ta daga wannan kasa tamu ta hanyar shiga lunguna da kauyuka domin fadakar da al’umma yadda cutar take da kuma hanyoyin kariya daga kamuwa da ita bisa binciken masana ilimin cutar.”