An yi taron addu’ar tunawa da Fadar Bege
A cikin wannan makon ne shahararren mawakin Musuluncin nan Umar Abdul’aziz Baba wanda aka fi sani da Fadar Bege ya cika shekara daya da rasuwa, hakan ya sa takwarorinsa a fadin kasar nan suka yi cikar farin dango a Jihar Kano don gudanar da addu’oi na musamamn gare shu.Baya ga addu’oi an gudanar da tarurruka […]
A cikin wannan makon ne shahararren mawakin Musuluncin nan Umar Abdul’aziz Baba wanda aka fi sani da Fadar Bege ya cika shekara daya da rasuwa, hakan ya sa takwarorinsa a fadin kasar nan suka yi cikar farin dango a Jihar Kano don gudanar da addu’oi na musamamn gare shu.
Baya ga addu’oi an gudanar da tarurruka daban-daban da suka hada da wa’azi da saukar Alkur’ani Mai tsarki da kuma gudanar da majalisi a wurare daban-daban, haka kuma an kai ziyara ta musamman ga ainihin Fadar Bege da ke Wudil wanda a nan mamacin ya samo sunansa.
A lokacin da yake jawabi a wajen wa’azin da aka gudanar don tunawa da marigayin, malaminsa Shaik Sharif Sani Janbulo ya bayyana muhimmancin hadin kan Musulmi, inda ya ce bai dace a rika jifan duk wani Musulmin da ya yarda da Allah da miyagun kalmomi ba.
Ya ce Fadar Bege ya bayar da gudunmawa kwarai da gaske wajen wayar da kan Musulmi game da son Annabi (SAW), inda zuwan wakokinsa ne ya sa matasa suka daina sauraren wakokin fina-finan Indiya.
Ya shawarci mawakan Musulunci su rika neman ilimin addini da sanin wanda za su yi wa bege kafin su rika yin wakarsu.
Hafiz Abdallah wani mawaki ya yi kira ga mawaka da su kwaikwayi Fadar Bege, kada su yarda wani abu na duniya ya rude su har su bar abin da suke yi don Allah.
Ya ce mawaka za su yi amfani da wannan taron don tattauna abubuwan da suka shafe su da kuma ganin an samu hadin kai da kuma yadda za su ci gaba wajen tunkarar manufar da suka sa a gaba ta yin wakar Annabi (SAW).
Wani na kusa da Fadar Bege mai suna Muktar Muzajjabi wanda suke tare tun marigayin yana garin Wudil har zuwa lokacin dawowarsa Kano, wanda kuma ke kula da wurin daukar wakoki na Labbaika Studio wanda kamfanin na marigayin ne, ya ce abotarsu da marigayin ta samo asali ne sakamakon kaunar da suke yi wa manzon Allah (SAW).
Mai dakin marigayin Malama Ramlah Hafis kofar Mazugal ta ce tana yi wa marigayin mijin nata fatan samun shiga Aljannar Firdausi da kuma haduwa da Manzon Allah (SAW).