An yi taron kaddamar da albam din yabon Manzon Allah a Kano
A makon jiya ne aka kaddamar da albam din wakokin yabon Manzon Allah (SAW) mai suna ‘Uzuri’ na mawaki Salisu Malam-malam Gaya a Kano. Wannan shi ne karo na farko da aka taba kaddamar da albam din yabon Manzon Allah (SAW).Albam din mai wakoki hudu- ‘Ya Zo Ya Tafi’ da ‘Sayyada’ da Ladabi’ da kuma […]
A makon jiya ne aka kaddamar da albam din wakokin yabon Manzon Allah (SAW) mai suna ‘Uzuri’ na mawaki Salisu Malam-malam Gaya a Kano.
Wannan shi ne karo na farko da aka taba kaddamar da albam din yabon Manzon Allah (SAW).
Albam din mai wakoki hudu- ‘Ya Zo Ya Tafi’ da ‘Sayyada’ da Ladabi’ da kuma ‘Uzuri’ an kaddamar da shi ne a babban dakin taro na gidan Mambayya da ke Unguwar Gwammaja a Birnin Kano.
Kamfanin Ambato Foundation da hadin gwiwar A & Y Enterprise ne suka dauki nauyin bikin.
Mataimakin Gwamnan Jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje da Sakataren Gwamnatin Jihar Kano, Rabi’u Suleiman Bichi da Sanata Kabiru Ibrahim Gaya da dan Majalisar wakilai ta tarayya, Abdurrahman Kawu Sumaila sun halarci bikin.
Shahararen mawaki Hafiz Abdullah ne ya wakilci Sayyadi Shariff Sani Janbulo a wurin bikin.
kungiyar Jama’atu Ahbabu Rasulullah, karkashin jagorancin Sayyadi Shariff Sani Janbulo ta sayi kwafi 50 na albam din a kan Naira dubu 500. Hafiz Abdallah ya ba mawakin kyautar kujerar Makka.
Mai kaddamarwa, Mataimakin Gwamnan Jihar Kano, Abdullahi Ganduje, ya sayi kwafi 20 kan Naira dubu 300, sai Sakataren Gwamnatin Kano, Rabiu Bichi ya sayi nasa kwafin kan Naira dubu 200. Shugaban karamar Hukumar Dala da kansilolinsa da mutanen Dala, suka sayi kwafi 50 kan Naira dubu 200.
Sanata Kabiru Gaya ya sayi kwafi a kan Naira dubu 100. dan majalisar tarayya mai wakiltar karamar Hukumar Dala, Aliyu Sani Madakin Gini ya sayi kwafi daya kan naira 100.
kananan Hukumomin Kura da Gwale kowacce ta sayi kwafi daya a kan Naira dubu 50. Iyalin Mai Kifi, sun sayi nasu kwafin ta hannun Mai ba Gwamnan Jihar Kano Shawara kan harkokin mata Hajiya Fatima Dala, a kan Naira dubu 200. Hon. Kawu Sumaila ya saya kan naira dubu 100.
kungiyar Kainuwa da Hon. dan Maliki kowanne ya saya a kan Naira dubu 100, tsohon Shugaban karamar Hukumar Nasarawa, Nasir Gawuna ya saya a kan Naira dubu 50.
A farkon bikin ne manyan malamai suka gabatar da kasidu, sannan wasu daga cikin mawakan da suka halarci taron suka rera wakokin yabon Ma’aiki (SAW).
Mawakin Salisu Malam-Malam ya gode wa wadanda suka ba da gudunmawa ko suka halarci taron.