An yi taron koli kan noman albasa a Katsina
Kungiyar Masu Sa ido kan Sha’anin Albasa ta Afirka ta Yamma da Afirka ta Tsakiya (ORO) tare da hadin gwiwa da Kungiyar Manoma Albasa da Kasuwancinta ta Najeriya sun yi taro na farko a bana a Jihar Katsina. An gudanar taron ne da nufin farfado da rashin tsari kan kamfanonin sarrafa albasa a kasashen Afirka […]
Kungiyar Masu Sa ido kan Sha’anin Albasa ta Afirka ta Yamma da Afirka ta Tsakiya (ORO) tare da hadin gwiwa da Kungiyar Manoma Albasa da Kasuwancinta ta Najeriya sun yi taro na farko a bana a Jihar Katsina. An gudanar taron ne da nufin farfado da rashin tsari kan kamfanonin sarrafa albasa a kasashen Afirka ta Yamma da Afirka da ta Tsakiya da suke fama da shi. Akwai kungiyoyin noman albasa a tsakanin kasashe 22 da ke noman albasar.
Taron ya samu halartar wakilan kasashen Benin da Cote d’iboire da Ghana da Mali da Najeriya da Nijar da kuma Togo.
Gwamnan Jihar Katsina, Alhaji Aminu Bello Masari, wanda ya samu wakilcin Mai ba shi Shawara ta Fuskar Kasuwanci, Alhaji Abubakar Yusuf, ya ce Jihar Katsina, jihar manoma ce wadda ke da akalla kashi 80 cikin 100 na manoman auduga da gyada da masara da gero da dawa da sauransu.
Ya ce jihar ta shahara a wajen noma kayan lambu wanda ake fitar da su zuwa kasashen waje; tun kafin 1960 inda albasar da kowa ya san amfaninta na daga ciki.
Gwamna Masari ya ce: “Jihar Katsina na da kasar noma kimanin kadada miliyan 2.4, amma kadada miliyan 1.6 ake nomawa, saura dubu 800 na nan a matsayin fili. Har ila yau, akwai madatsun ruwa 80 da ke dauke da ruwa kwatankwacin murabbain lita miliyan 1.121 domin noman rani,” inji shi.
Ya ce noman albasa zai kara bayar da damar samar da ayyukan yi a tsakanin al’umma da kuma kara habaka tattalin arzikin kasa.
“Kazalika, Gwamnatin Jihar ta samar da wani kwamiti a kan hadin gwiwa da kamfanoni domin inganta harkokin noma. Har ila yau, an samar da masu horarwa a kan harkar noma a dukkan mazabun da ke jihar. Sa’annan gwamnati za ta ci gaba da yin nazari a inda ake samun wasu matsaloli domin shawo kansu domin gaba. Kuma gwamnati na shirye ta tallafa wa noman albasa a duk fadin jihar,” inji wakilin Gwamnan.
Kwamishinan Ayyukan Gona na Jihar, wanda kuma shi ne Mataimakin Gwamnan Jihar, Alhaji Mannir Yakubu, wanda ya samu wakilcin Mai bayar da Shawara a kan Ayyukan Gona, Dokta Abba Yakubu Abdallah, ya ce za a gina masakar hadin gwiwa a tsakanin Gwamnatin Jihar da Ma’aikatar Masana’antu da Kasuwanci da ta Tattalin Arziki ta Tarayya kuma har gwamnati ta kebe fili kadada 140 don wancan aiki. Ya ce irin wannan yunkuri ko shakka babu za a yi wa manoman albasar irinsa domin bunkasa nomanta da sauran kayan gona da na lambu domin tabbatar da cewa Najeriya ta rike kambunta a wajen samar da albasar a Afirka ta Yamma da Afirka ta Tsakiya.
Ya kara da cewa, domin ganin an habaka noman albasa a jihar, tuni gwamnatin ta shigar da Kungiyar Manoman Albasa a cikin shirin Anchor Borrwers na Babban Bankin Najeriya. A kan haka ne, ya yi fatar samun musayar ra’ayoyi a tskanin kwararrun da suka fito daga sassan Afirka kuma suka halarci wannan taro don amfanar da manoma.
Shugaban Kungiyar ORO ta Afrika, Alhaji Mustafa Kadiri, ya ce, wannan kungiya tasu na da manufar farfado da darajar noman albasa tare da habaka harkokin kasuwancinta. Sannan sun zabi Jihar Katsina ce don su yi taron kungiyar na farko na 2020 ne tun a taron da suka yi a Sakkwato a bara bisa la’akari da muhimmancin da jihar ke da shi, musamman lura da yadda Gwamna Masari ke ba harkar noma muhimmanci. Ya ce, “Akalla ana bukatar tan miliyan 1.2 na albasa daga Najeriya; sai dai har yanzu tan miliyan 1.1 ake samu, inda Jihar Sakkwato ke kan gaba wajen samar da albasar, sai Kebbi da Kano da Kaduna, yayin da Katsina da Zamfara da sauransu ke biye.”
Ya ce masana albasar sun kasa kasuwancin albasar gida uku, wato cinikin kasuwanni na yau da kullum, sai kasuwancinta da ake yi tsakanin yankuna ko bangarori, kamar su Nijar da Mali da sauransu, sa’nnan sai kasuwancin kamfanoni, kamar na masu yin taliyar Indomie ko Nestle da sauransu, wadanda ke bayar da tsari da kuma irin yanayin albasar da suke so.
Mista Koffi Komenel shi ne Shugaban Kungiyar a Kasar Kwaddebuwa (Cote de’iboire) ya ce, duk wani lamarin da aka ce Najeriya ta shiga cikinsa to lallai abu ne mai muhimmanci sosai. Saboda haka, kasarsa tana bukatar Najeriya ta je can domin ta rika noma albasar.
Takwaransa na Togo, Mista Kussi Pius, damuwar kasarsa ya nuna kan rashin samar da wajen ajiyar albasa a kasar kamar yadda wasu kasashen suka yi. Saboda haka, ya yi kira ga Najeriya ta fara kai albasa a kasar tunda ta fi sauran kasashen nomanta.
Shugaban Kungiyar Manoma ta Jihar Katsina, kuma Kwamishinan Kananan Hukumomi da Masarautu, Alhaji Ya’u Umar Gwajo-Gwajo, ya yi kira ga manoman da suka karbi bashin shirin Bankin CBN na Anchor Borrower su tabbatar sun yi amfani da kudin domin yin noma. “Kada mutum ya ga ya karbi wadannan kudi ya je ya yi ta hidimar gabansa, bayan bashi aka ba shi ba kyauta ba, kuma ake sa ran zai maido a kan wa’adin da aka yi da shi domin bai wa wadansu,” inji shi.
Ya ce, kungiyar za ta ci gaba da sa ido don ganin an yi amfani da kudin kamar yadda ya dace.
Shugabannin Kungiyar ORO da suka halarci taron, sun hada da Alhaji Mustafa Kadiri Shugabanta na Afirka ta Yamma da Afirka ta Tsakiya, da wakilin na Najeriya Dokta Muhammad Ali Inname, sai Alhaji Aminu Haruna daga Nijar. Sauran sun hada da Bala Haruna daga kasar Benin, sai Mme Kady Camara daga Mali da Mista Koffi Kamenal daga Cote d’iboire sai Mista Kussi Pius daga kasar Togo tare da mai masaukin baki, Alhaji Umar Shirwa.