An yi taron Maulidin ƙasa duk da gargaɗin harin ’yan ta’adda a Kano

Taron Maulidin karo na 39 ya samu halarcin Mataimakin Shugaban Kasa Kashim Shettima.

An yi taron Maulidin ƙasa duk da gargaɗin harin ’yan ta’adda a Kano

An gudanar da taron Maulidin ƙasa duk da gargaɗin da ’yan sanda suka yi kan barazanar harin ’yan ta’adda a Jihar Kano.

Aminiya ta ruwaito cewa, ’yan ɗariƙar Tijjaniyya daga sassan Nijeriya daban-daban sun halarci taron Maulidin na Shehu Ibrahim Inyas na shekara-shekara da aka gudanar a Filin Wasa na Sani Abacha da ke ƙwaryar Birnin Dabo.

Sai dai tun a jiya Juma’a ce mai magana da yawun ’yan sandan Kano, Abdullahi Haruna Kiyawa ya fitar da sanarwa mai ɗauke da gargaɗin cewa ’yan ta’adda na shirin kai hari a jihar saboda haka jama’a su ƙauracewa duk wani taro da shiga cunkoso.

Daga bisani Kwamishinan Labarai na Jihar Kano, Abdullahi Waiya, ya fitar da sanarwar cewa babu makawa sai taron ya gudana.

Ya ƙara da cewa gwamnatin jihar ba ta da labarin wata barazanar tsaro, don haka babu dalilin dakatar da taron ko tunanin mugun abu zai faru a wurin taron wanda aka shafe shekaru 39 ana gudanarwa duk shekara da mahalarta daga duk faɗin Nijeriya kuma an cika ka’idoji wajen shirya shi bana.

Bayan wannan martani da Kwamishinan ya yi ne rundunar ’yan sandan ta lashe amanta da cewa za ta bayar da cikakken tsaro a wurin taron.

Taron Maulidin karo na 39 ya samu halarcin Mataimakin Shugaban Kasa Kashim Shettima wanda ya jinjina wa ’yan ɗariƙar Tijjaniyya da suka kasance jakadun haɗin kai a tsakanin al’ummar Musulmi.

Shettima wanda ya kasance babban baƙo a yayin taron, ya bayyana ɗarikar Tijjaniyya a matsayin wadda ta yi tsayin-daka wajen koyar da addinin Islama a bisa tafarki madaidaici tsawon shekaru da dama.

Shettima wanda Babagana Fannami ya wakilta, ya jaddada irin jajircewar da ɗariƙar Tijjaniyya ta yi wajen koyar da kyawawan ɗabi’u na fiyayyen halitta Annabi Muhammad (SAW).

A nasa ɓangaren, Gwamna Abba Kabir Yusuf wanda ya kasance mai masaukin baƙi a yayin taron, ya yaba wa ɗariƙar Tijjaniyya musamman dangane da tabbatar da haɗin kai tsakanin sauran ɗariƙu a ƙasar.

Sarki Muhammadu Sanusi II wanda kuma shi ne shugaban ɗariƙar Tijjaniyya a Nijeriya, ya yi addu’ar haɗin kan musulmi a duniya tare da sauran mabiya addinai da aƙidu daban-daban.

Mataimakin Gwamnan Kwamared Gwarzo da Sarki Sanusi II da Gwamna Abba Kabir a wurin taron Maulidin