An yi taron sasanta manoma da makiyaya a Ekiti
A ranar Talatar da ta gabata ce aka gudanar da taron sasanta Fulani makiyaya da manoma a fadar Ewi na Ado Ekiti da ke Jihar Ekiti. Taron da aka shirya a karkashin jagorancin Mai alfarma Sarkin Musulmi da Gwamnatin Jihar, an ba manoman damar fayyace barnar da suke ikirarin Fulani makiyaya na yi musu a […]
A ranar Talatar da ta gabata ce aka gudanar da taron sasanta Fulani makiyaya da manoma a fadar Ewi na Ado Ekiti da ke Jihar Ekiti.
Taron da aka shirya a karkashin jagorancin Mai alfarma Sarkin Musulmi da Gwamnatin Jihar, an ba manoman damar fayyace barnar da suke ikirarin Fulani makiyaya na yi musu a gonakinsu, domin samar da maslaha.
daya daga cikin manoman da suka halarci taron, Alhaja Aminat Bello, kokawa ta yi bisa yadda makiyayan suka yi mata dirar mikiya a gonarta, inda suka lalata ilahirin amfanin gonar. Ta gabatar da shaidun hotuna da na bidiyo na ire-iren barnar da aka yi mata, wadanda suka nuna yadda Fulanin ke hakar rogo a gonarta suna ba dabobbinsu. Hakazalika shugaban kungiyar Manoma ta Jihar, Omoyajowo John ya koka bisa yadda Fulani makiyayan ke janyo masu gagarumar asarar a duk shekara, inda ya bukaci a gaggauta daukar kwararan matakai domin samar da maslaha.
Kwamishinan Gona da Raya Karkara na Jihar Ekiti, Kehinde Odebunmi ya shaida wa Aminiya cewa bisa la’akari da yawan korafe-korafen da manoman jihar ke yi, kan barnar da Fulani makiyaya ke yi musu a gonakinsu ya sanya su kai kukansu ga Mai alfarma Sarkin Musulmi, wanda ya ba da umarnin a shirya taron bin bahasi da neman mafita a karkashin jagorancin Iwi na Ado Ekiti, Oba Rufus Adeyemo, taron da ya ce ya yi armashi matuka, domin an tattauna muhimman al’amura cikin kwanciyar hankali da fahimtar juna.
Shugaban kungiyar Fulani Makiyaya ta Miyyeti Allah, Alhaji Muhammadu Kirwa, Hardon Zuru, ya bayyana damuwarsa bisa koke-koken da manoman suka gabatar ya kuma sha al’washin daukar kwararan matakan da suka dace domin ganin ba a ci gaba da cutar da su ba. “Koken da suka yi abu ne na tausayawa, abu ne na bakin ciki da tayar da hankali kuma a jagorancin da muke yi, ba za mu yarda mu daure wa karya gindi ba. Ba za mu lamunce wa duk wani mai kokarin kawo barazana ga zaman lafiyar Jihar Ekiti da Najeriya ba,” inji Hardon.
A nasa bangaren, babban basarake mai daraja ta daya a jihar ta Ekiti, Oba Rufus Adeyemo Adejugbe Aladesanmi III, kira ya yi ga Fulani makiyaya da manoman su rungumi akidar zaman lafiya, domin a cewarsa dukanninsu ’yan uwan juna ne bisa la’akari da shekaru aru-arun da suka yi a jihar ba tare da jawo wata fitina ba.