An Yi Tiyatar Ƙoda ta Saman Fata Ta Farko A Kano

An gudanar da tiyatar ciwon ƙoda da yoyon fitsari ta hanyar amfani da fasahar Hasken Radiation (LASER) da ake yi ta saman fata a Asibitin Koyarwa na Aminu Kano (AKTH).  An samu nasarar yin wannan aiki ne da agajin Asusun Bada Tallafi Na Manyan Makarantu a Najeriya (TETFund). TETFund ya samar da kayan aiki ga […]

An Yi Tiyatar Ƙoda ta Saman Fata Ta Farko A Kano

An gudanar da tiyatar ciwon ƙoda da yoyon fitsari ta hanyar amfani da fasahar Hasken Radiation (LASER) da ake yi ta saman fata a Asibitin Koyarwa na Aminu Kano (AKTH). 

An samu nasarar yin wannan aiki ne da agajin Asusun Bada Tallafi Na Manyan Makarantu a Najeriya (TETFund).

TETFund ya samar da kayan aiki ga AKTH sannan ya tattaro likitoci daga asibitocin jihohi shida na Arewacin Najeriya aka ba su horon kan aiki yadda ya kamata da sabbin na’urori da ke amfani da fasahar laser.

Wani ƙwararren likita daga ƙasar Poland, Dokta Przemyslaw Zugaj da ya jagoranci aikin, ya ce za a iya amfani da sabbin kayan aikin wurin tiyatar cututtuka masu rikitarwa da suka hada da koda, mafitsara da da sauransu.

Ya ce, fasahar laser za ta sauƙaƙa wa marasa lafiya jinya da zaman asibiti domin yana da saurin warkewa, tunda ba yanka jikin majinyaci ake yi kamar yadda aka saba tiyata ba.

Farfesa Sani Aji daga Jami’ar Bayero ta Kano, ya jaddada alfanun da ke tattare da tiyatar Laser, inda ya ce, majiyyata ba sa bukatar a yi musu manyan allurai ko kuma tsawaita musu zama a asibiti kamar yadda ake yi a da.

Farfesa Samuel Osaghae na Jami’ar Benin ya bayyana jin daɗinsa ga wannan shiri na TETFUnd, inda ya ce samun kayan aikin zai inganta tiyatar yoyon fitsari da kuma yin tasiri mai kyau wurin samar da kiwon lafiya a Najeriya.

Dakta Haruna Usman na Jami’ar Abubakar Tafawa Balewa da ke Bauchi ya ce za a samu sauƙin kashe kuɗi, kuma marasa lafiya za su samu sauƙin al’amura.

Ya ce, tiyatar Laser na rage bukatar manyan magungunan kasashen waje masu tsada, zai kuma kawar da wahalar tafiye-tafiye neman lafiya.