An yi tsafi da zabaya 74 a kasar Tanzaniya -Rahoto
A wani rahoto da majalisar dinkin duniya ta fitar ta bayyana an sace hade da kashe zabaya 74 a kasar Tanzaniya daga shekarar 2000 zuwa 2014 don yin tsafi da su. Majalisar ta fitar da rahoto ne sakamakon wani jariri zabaya da aka sace a yammacin kasar Tanzaniya a ranar Lahadi.’Yan sanda sun bayyana an […]
A wani rahoto da majalisar dinkin duniya ta fitar ta bayyana an sace hade da kashe zabaya 74 a kasar Tanzaniya daga shekarar 2000 zuwa 2014 don yin tsafi da su.
Majalisar ta fitar da rahoto ne sakamakon wani jariri zabaya da aka sace a yammacin kasar Tanzaniya a ranar Lahadi.
’Yan sanda sun bayyana an sace zabaya dan shekara 1 mai suna Yohana Bahati, bayan wadansu bata-gari sun shiga gidan mahaifansa, sannan suka sari mahaifiyarsa da adda.
A yanzu an samu gawar jaririn ne a bayan gari, inda aka sare masa hannuwansa.
An kama mutane biyu da ake zargin suna da alaka da sace jaririn.
Ana amfani da sassan jikin zabaya wajen tsafe-tsafe a kasar, musamman don samu nasara a siyasa.
A watan Disamba 2014 ne kasar ta kafa dokar hukunta duk wanda aka samu da laifin sace hade da yin garkuwa da zabaya a kasar.
Mai magana da yawun ’yan sanda a yammacin kasar, Joseph Konyo ya ce, suna bincike kan al’amarin, inda a yanzu suke yi wa mahaifin jaririn tambayoyi.
“Har yanzu muna farautar wadanda suka sace shi, mun kuma bukaci mutane su ba mu hadin kai don mu cafke wadanda suke da hannu a cikin. Akwai mutane biyu a hannunmu da ake zargi da hannu wajen sace jaririn.” Inji Mista Konyo.
Idan ba a manta ba a wani rahoto da ma’aikatar lafiya ta kasar Tanzaniya ta fitar a shekarar 2006, ta ce akwai yiwuwar a haifi zabaya 1 a cikin jarirai 1,400 da za a haifa.
Sace-sacen zabaya na karuwa a kasar ne sakamakon wata al’ada da mutanen kasar suke da ita, cewa za su samu biyan bukata cikin gaggawa ta hanyar tsafi da zabaya. Hakan ya sanya majalisar dinkin duniya a watan Agustar bara ta bayyana sace-sacen zabaya na karuwa sakamakon karatowar zabuka a kasar.
Matsafa kan sayi zabaya da tsada inji kungiyar bada agaji ta Red Cross da ke kasar.
’Yan sanda a kasar sun ce akan sayar da sassan jikin zabaya a kan Dala dubu 75.
A watan Disamba 2014 ’yan sanda a kasar sun ce akwai kyauta mai gwabi ga duk wanda ya samar da bayanin da zai sa a samu wata zabaya da aka sace a kasar.