An yi tseren ‘Olympic’ don inganta lafiyar jama’a a Gombe

Gwamnatin jihar ta ce manufar shirya taron shi ne samar da al’umma mai cike da lafiya.

An yi tseren ‘Olympic’ don inganta lafiyar jama’a a Gombe

Gwamnatin Jihar Gombe, ta hannun Ma’aikatar Matasa da Ci gaban Wasanni, ta gudanar da Tseren Motsa Jiki na Olympic na shekarar 2026 a Filin Wasanni na Pantami da ke jihar.

An shirya taron ne domin ƙarfafa mutane su rungumi motsa jiki, inganta lafiya da kuma ƙara haɗin kai a tsakanin al’umma.

Mutane daga sassa daban-daban na jihar sun halarci taron.

Da yake jawabi, Daraktan Wasanni na ma’aikatar, Manga Sale, ya ce shirin na da nufin ƙarfafa jama’a su yi rayuwa mai cike da motsa jiki tare su kuma rungumi wasannin Olympics.

Ya bayyana cewa wasanni ba wai don gasa kawai ake yin su ba, suna kuma taimakawa wajen haɗa kan jama’a, inganta lafiya da kuma gina al’umma mai ƙarfi.

Shi ma Babban Mataimaki na Musamman ga Gwamna kan Harkokin Matasa da Wasanni, Hon. Bappah Gombe Abdullahi, ya yaba wa mahalarta taron bisa fitowarsu da suka yi.

Ya buƙaci al’ummar jihar su mayar da motsa jiki wani ɓangare na rayuwarsu ta yau da kullum domin samun ingantacciyar lafiya.

Ya kuma tabbatar da cewa gwamnatin Gwamna Muhammadu Inuwa Yahaya za ta ci gaba da tallafa wa matasa da shirye-shiryen da ke bunƙasa harkokin wasanni da inganta rayuwa mai ƙoshin lafiya.

Ana gudanar da Ranar Olympic a kowace shekara a ƙasashe daban-daban domin ƙarfafa jama’a su kasance masu motsa jiki tare da amfani da wasanni wajen ƙarfafa haɗin kai da zaman lafiya.