An yi wa agwagwa sabon takalmi saboda ciwo a kafar
Wani likitan dabbobi a garin Tennessee mai suna John Didon ya yi wa wata agwagwa takalmi da abin hada tabarma. Agwagwar da ake kira da Jenny, likitan asibitin dabbobi na Rocky Top, Dokta Matt Kuillen, ya ce wanda ya mallaki Jenny ya fahimcewa idan agwagwar na tafiya tana dingisawa don haka ya nema mata takalmin […]
Wani likitan dabbobi a garin Tennessee mai suna John Didon ya yi wa wata agwagwa takalmi da abin hada tabarma.
Agwagwar da ake kira da Jenny, likitan asibitin dabbobi na Rocky Top, Dokta Matt Kuillen, ya ce wanda ya mallaki Jenny ya fahimcewa idan agwagwar na tafiya tana dingisawa don haka ya nema mata takalmin da zai taimaka mata idan tana tafiya.
Dokta Matt, ya ce agwagwar tana dauke da larurar “bumblefoot,” da ke sa ba ta iya tafiya ko’ina.
“Wannan agwagwar tana yawan jin zafi a tafin kafarta idan tana tafiya,” Kamar yadda Dokta Matt ya bayyana wa gidan talabijin na WCYB-TB.
Dokta Matt, ya ce John ya yi amfani da tabarmar kicin ne ya hada wa Jenny takalmin da zai taimaka mata wajen cutar da take damunta. “Na hada wa Jenny takalmin ne don rage radadin zafin ciwon da take yawan yi koyaushe idan tana tafiya,” inji shi.
Asibitin dabbobin sun wallafa bidiyon Jenny tana tafiya da sabon takalminta, wannan sabon takalmi da John ya hada wa Jenny ya wuce tunanin yadda wasu ke zaton za su kalli sabon takalmin.