An yi wa Arewa duk abin da za a yi mata

Yau za mu bada dama ga daya daga cikin masu aiko mana da gudunmawar rubutu wato Kwamared Bishir Dauda Sabuwar Unguwa wannan fili ne domin yin sharhi kan halin da Arewa take ciki kamar haka: Yanzu dai duk abin da za a yi wa Arewa an riga an yi, sai dai a dada da kari. […]

An yi wa Arewa duk abin da za a yi mata
An yi wa Arewa duk abin da za a yi mata

Yau za mu bada dama ga daya daga cikin masu aiko mana da gudunmawar rubutu wato Kwamared Bishir Dauda Sabuwar Unguwa wannan fili ne domin yin sharhi kan halin da Arewa take ciki kamar haka:

Yanzu dai duk abin da za a yi wa Arewa an riga an yi, sai dai a dada da kari. An kashe mutane bila adadin, an kone dukiya, an ci zarafin mutane.To me kuma ya rage? Kuma duk wannan abin da ke faruwa, har yanzu Gwamnatin Tarayya gani take ba laifinta ba ne. Kullum idan an kashe mutanen Arewa, sai gwamnati da ’yan kazaginta da wasu mutanen Kudu su fito su kare gwamnati. Wani mutumin kasar Austreliya mais una Stephen Dabis da kwanakin baya  ya fito da sakamakon bincikensa, ya ce tsohon Gwamnan Jihar Borno Ali Modu Sharrif da tsohon Hafsan Sojan Najeriya Janar Ihejirika ne ke ba kungiyar ’yan Boko Haram da ke cin karensu ba babbaka a Arewa maso Gabas tallafi da goyon baya. Gwamnati da masu ci daga jikinta suka fito suka karya ta shi. Ciki har da Hukumar Tsaron kasa (SSS) inda ta yi rawar gaban hantsi ma ta ce babu ruwan Ihejirika amma da ruwan Modu Sharrif. Wannan wankewa da Hukumar SSS ta yi ya zo daidai da harshen Gwamnatin Tarayya. Kada mu manta har yau, tunanin Shugaban kasa shi ne, wai kungiyar Boko Haram wasu ‘yan siyasar Arewa ne suka bijiro da ita domin su hana shi gudanar da mulki. Wannan yas a gwamnatinsa ke wa batun rikon sakainar kashi, wai a tunaninsu, a bar matsalar ta ci gaba da cinmu tunda sun gano Musulmin Arewa ne ta fi shafa. Saboda abin nan ne da Bahaushe kan kira alhaki kuikuyo mai shi yake bi.Wato mu ’yan Arewa mun gina masa ramin mugunta kuma mun fada!
To, sai dai duk da wasa da hankali da gwamnatin ke wa ’yan Arewa an gano su, kuma duk an gano makarkashiyar, hatta kawayen gwamnatin irin su Amurka, kallon hadarin kaji kawai take musu, kuma lokaci ne kawai zai nuna wane mataki duniya za ta dauka kan gwamnatin Jonathan.
Domin dai duniya ba za ta kyale burin wani ko wasu ’yan tsirarrun mutane su ruguza Afirka ba. Abin da ya sa na ce Afirka shi ne dubi girman Najeriya da yawan al’umarta, kuma dubi illar rugujewarta a Nahiyar Afirka. Kada mu manta Najeriya ita ce kasa mafi yawan mutane a Afirka kuma mafi yawan bakar fata a duniya. Don haka rushewarta babban bala’i ne a duniya. Sai dai tilas a gaggauta kawo karshen wannan gwamnati, domin tuni wasu sassa na kasar suka fada hannun ’yan bindinga. Garuruwan Gwoza da Gamborun Gala da Bama da sauransu duk sun koma karkashin ikon ’yan ta’adda. Don haka ya zama tilas Amurka ta ba da goyon baya a kawar da gwamnatin da ke wasa da makomar ’yan kasarta.
Da ma baya ga matsalar ’yan ina-da-kisa, baki dayan Arewa cikin rikici take.Tun daga Zamfara mai tarin barayin shanu zuwa Birnin Gwari da ke fama da harin gaggan ’yan fashi da ake kai wa makamai cikin jirgi mai saukar ungulu zuwa Wukari inda ake ta zubar da jini da sunan kabila da addini zuwa Binuwai da Nasarawa inda ’yan bindigar kabilar Eggon suka sa zare da makiyaya da sauransu. Wannan duk na nuna yadda gwamnati da gangan ta kyale mu rusa yankin.
Sai dai duk da makiyanmu na waje, wato Jonathan da ’yan uwansa akwai munafukai a cikinmu da ke daure masa gindi da sunan PDP. Wadannan munafukai wai har Majalisar Dattawan Arewa suka kirkiro inda suke kare Jonathan. Abin bakkin ciki shugaban wannan kungiyar dan Jihar Kano ne, kuma da shi aka hada kai ake cin amanar al’ummar Arewa.
Akasarin mutanen Arewa sun yi Allah wadai da wannan kungiya, domin sam wannan kungiya ba ta wakiltar jama’ar Arewa. Idan mutum ya kalli kungiyar tsaf da idon basira, zai ga manufarta tallata Shugaba Goodluck Jonathan ne domin ya kara zama Shugaban kasa a shekarar 2015. Kazalika kungiyar ta fito ne domin ta kara raba kan ’yan Arewa, idan aka yi la’akari da yadda a koyaushe take kalubantar kungiyar Dattawan Arewa da su Farfesa Ango Abdullahi ke jagoranta.
Bambancin dai a bayyane yake, domin kungiyar su Farfesa Ango Abdullahi ita ce ke magana, ita ce ke kare muradun Arewa ba na wadannan ’yan tsirarru ba. Ita dayar tana kare muradun Shugaba Jonathan ne da Mataimakinsa Namadi Sambo. Mu kuma talakawan Arewa mun san su wane ne dattijai na hakika a Arewa, mun kuma san wadanda ke neman abinci.
Wadanda suka tafi wajen Goodluck da Namadi, aka hada kai da su domin sayar da al’ummar Arewa, su sani hakan ba zai haifar masu da da mai ido ba, domin yau dai ga halin da Arewa take ciki, tuni ma ’yan gudun hijira daga jihohin Arewa maso Gabas suka fara kwarara Jihar Kano, don haka kowa zai gaya musu.Yanzu Arewa tana neman dattawa na hakika irin su Maitama Sule da Farfesa Ango Abdullahi da Paul Unongo da Barista Solomon Dalung da Alhaji Abdulkarim dayyabu da sauransu. Wadannan mutane ya kamata in sun fada mu bi, kuma su ne abin biyayya wadanda za su iya jagorantar Arewa don kare mutuncinta.
’Yan Arewa dole mu kara hade kanmu, idan muna son mu ci nasara a wannan gwagwarmaya. Mu zama masu magana da murya daya. Mu tuna da irin gwagwarmayar da su Firimiya Sa Ahmadu Bello suka yi wajen kare mutuncin Arewa da al’ummarta inda a karshe sai da suka biya da rayukansu. To, irin wannan tunani ne ya kamata a ce kowane dan Arewa nada shi a wannan lokaci.
Allah Ya kare Arewa da al’ummarta baki daya, amin.
Kwamared Bishir Dauda Sabuwar Unguwa Katsina Babban Sakataren kungiyar Muryar Talaka ta kasa. 08165270879