An yi wa Bajamushe allurar Covid-19 sau 217 ba ta yi tasiri ba

An yi wa wannan mutumin waɗannan allurai har sau 217 a cikin watanni 29. 

An yi wa Bajamushe allurar Covid-19 sau 217 ba ta yi tasiri ba

Mujallar cututtuka ta Lancet ta ruwaito cewa an yi wa wani Bajamushe mai shekaru 62 allurar rigakafin murar sarkewar numfashi (Covid-19) sau 217. 

Kamar yadda mujallar Saudi Gazete ta bayyana, masu bincike kan kiwon lafiya daga Jami’ar Erlangen-Nuremberg sun ce, an yi wa wannan mutumin waɗannan allurai har 217 a cikin watanni 29. 

Dokt Kilian Schober, daga sashen nazarin halittu na jami’ar ya ce, “Mun sami labarin lamarinsa ta hanyar jaridu.

“Mun tuntube shi kuma muka gayyace shi don yin gwaje-gwaje daban-daban a Erlangen. Binciken ya nuna cewa mutumin na sha’awar a yi masa hakan.”

Dokta Schober ya ce, sun gayyaci mutumin, kuma ya amince su ɗebi jininsa domin gwaje-gwajen abin da ya sa aka riƙa yi masa allurar riga-kafin amma bai ji komai ba. 

A sabon binciken, an gwada daskararren jinin mutumin da aka ajiye a shekarun baya. 

Dokta Schober ya ce, “Mun sami damar ɗaukar samfurin jinin mutumin da kanmu, bayan ya nace sai an ƙara yi masa allurar har a lokacin da muke gudanar da binciken.”

Masu binciken sun sami damar yin amfani da waɗannan samfur ɗin jinin mutumin domin gano tasirin da rigakafin ke yi a jikinsa, amma basu ga komai ba.

Likitocin sun ce, allurar rigakafin COVID-19 ba za ta iya haifar da kamuwa da cutar ba, amma tana koya wa jiki yadda zai yaƙi cutar.  

Sun bayyana cewa, allurar rigakafi na aiki ta hanyar nuna wa garkuwar jikin ɗan Adam samfurin ƙwayoyin cuta ne daga ƙwayar halitta. 

Dokta Schober ya ce babu wani amfani da maimaita allurai zai iya yi a jikin ɗan Adam, sai ma dai ya gajiyar da garkuwar jiki.

Sai dai kuma wani abin mamaki, masu binciken ba su sami shaidar yawan alluran da aka yi wa Bajamushen kuma babu alamar cewa ya taɓa kamuwa da COVID-19.

Sun ce: “ba mu amince da yin allurar rigakafi a matsayin dabara don habaka karfin garkuwar jikin dan Adam ba.”

Fintiri ya ƙirƙiro sabbin masarautu 7 a Adamawa

Arewacin Najeriya bai dogaro da wani yanki ba – Ndume

Jagoran Syria ya sha alwashin kwance ɗamarar ƙungiyoyin da ke rike da makamai

Sojojin ruwa sun gina wa al’ummar Zariya asibiti kyauta