An yi wa Blatter wanka da jabun Daloli

A ranar Litinin da ta gabata ne wani mai wasan barkwanci dan asalin Birtaniya mai suna Lee Nelson ya yi wa Shugaban Hukumar kwallon kafa ta duniya (FIFA) wanka da jabun daloli a matsayin wata hanya ta nuna bacin ransa a kan dambarwar cin hanci da rashawa da ta sarke hukumar ta FIFA.Al’amarin ya faru […]

An yi wa Blatter wanka da jabun Daloli
An yi wa Blatter wanka da jabun Daloli

A ranar Litinin da ta gabata ne wani mai wasan barkwanci dan asalin Birtaniya mai suna Lee Nelson ya yi wa Shugaban Hukumar kwallon kafa ta duniya (FIFA) wanka da jabun daloli a matsayin wata hanya ta nuna bacin ransa a kan dambarwar cin hanci da rashawa da ta sarke hukumar ta FIFA.
Al’amarin ya faru ne a lokacin da shugaban ke gabatar da jawabi ga ’yan jaridu  a hedkwatar Hukumar FIFA da ke Zurich a ranar Litinin da ta wuce.  An ce mutumin mai wasan barkwanci ya shammaci jami’an tsaron da ke wurin ne inda ya shiga ba tare da izini ba, kuma da shigarsa ne sai ya nufi wajen da Blatter yake gabatar da jawabi.  An dauka mutumin yana da wani sako ne da zai isar ga shugaban Hukumar ta FIFA amma sai ya shammace shi inda ya antaya masa jabun daloli.  Nan take Blatter ya yi zumbur ya mike kuma ya bar kujerar da yake zaune inda ya nuna mamaki da kuma bacin ransa a kan al’amarin.
Nan da nan jami’an tsaro suka yi ram da Lee Nelson kuma suka yi waje da shi.  Sai dai bayan kura ta lafa ne Blatter ya sake komawa kan kujerar don cigaba da yin jawabi.
Sai dai kafin shugaban ya fita daga dakin taron an ji yana cewa “wannan abu da ya faru ba shi da nasaba da kwallo”.  Amma bayan kura ta lafa sai shugaban ya dawo yana fadin: “har yanzu ina raye, kuma guguwar tsunami ba ta tafi da ni ba”.  Wadannan kalamai tamkar mayar da martani ne ga mutumin da ya tozarta shi.
Idan za a tuna, Sepp Blatter dai ya sauka daga kan mukaminsa ne bayan dambarwar da ta sarke hukumar ta FIFA na zargin cin hanci da rashawa bayan da wasu jami’an Amurka suka tasa keyar wasu daga cikin jiga-jigan hukumar su kimanin 14 gidan kaso a tukumar da ake musu na yin sama da fadi a hukumar.
Yanzu hukumar ta yanke shawarar gudanar da sabon zaben hukumar ne a ranar 26 ga watan Fabrairun 2016 kuma Blatter ya tabbatar ba zai sake tsayawa takara ba.

’Yan sanda sun kashe ’yan fashi 3 a Binuwai

Mahara sun sace bsarake, sun harbi matarsa a ƙauyen Ondo

Sarkin Musulmi ya umarci a fara neman jinjirin watan Muharram

An tsinci gawar wata mata babu kai a Abuja