An yi wa budurwar da ta yi tatil da giya fyade a cocin Ogun

An yi mata fyaden ne yayin taron wani coci na shekara-shekara

An yi wa budurwar da ta yi tatil da giya fyade a cocin Ogun

Fyade

’Yan sanda a Jihar Ogun sun kama wani mai suna Gbenga Kolawole bisa zargin yi wa wata budurwa mai shekara 16 fyade bayan ta yi tatul da giya.

Bayanai sun nuna cewa lamarin ya faru da budurwar ne yayin wani taron cika shekara bakwai da wani coci ya shirya a Adubi da ke Jihar ranar 6 ga watan Nuwamba.

Kakakin Rundunar ’Yan Sandan Jihar, Omolola Odutola ne ya bayyana hakan ga manema labarai a Abeokuta, babban birnin Jihar.

Omolola ya ambato mahaifiyar yarinyar ma cewa ta kai ’yar tata ne wani shagon sayar da giya da ke yanki sannan ta kulle ta a ciki.

Sai dai an ambato ta tana cewa, “A nan ne Gbenga Kolawole, mai shekaru 32 ya yi amfani da damar wajen yi mata fyaden.

Sai dai Kakakin ya ce wani mai suna Sunday Ibrahim, mazaunin yankin ne ya yi ram da Gbenga lokacin da yake tsaka da aika-aikar.

“Tuni aka garzaya da wacce aka yi wa fyaden asibitin Ore-Ofe domin ta samu kulawar lafiya, yayin da shi kuma wanda ake zargin yanzu haka ya shiga hannu ana ci gaba da bincike a kan shi,” in ji Kakakin ’yan sandan.