An yi wa Buhari ihu a Maiduguri
Jama’ar da suka yi dandazon tarar shugaban Najeriya Muhammadu Buhari, tun da sanyin safiyar yau Laraba a Maiduguri babban birnin jihar Borno sun yi ta kwarara ihu suna cewa, “Ba ma yi” “Ba ma so”. Dandazon jama’ar sun yi wa shugaba Buhari, ihun ba ma yi ne a lokacin da ya kai ziyar jaje biyo […]
Shugaba Buhari a fadar Shehun Borno
Jama’ar da suka yi dandazon tarar shugaban Najeriya Muhammadu Buhari, tun da sanyin safiyar yau Laraba a Maiduguri babban birnin jihar Borno sun yi ta kwarara ihu suna cewa, “Ba ma yi” “Ba ma so”.
Dandazon jama’ar sun yi wa shugaba Buhari, ihun ba ma yi ne a lokacin da ya kai ziyar jaje biyo bayan tashin bamabamai da suka hallaka akalla mutune 30 a jihar a baya bayan nan.
Shugaba Buhari ya ziyarci birnin Maiduguri a kan hanyarsa ta dawowa daga birnin Addis Ababa na kasar Habasha, inda ya halarci tattaunawa kan matsalolin kasashen Afirka da suka hada da rikicin tsawon shekaru da ake fama da shi a kasar Libiya